Kasancewar Tinubu ba ya ƙin Igbo ne ɗansa Seyi ya auri ʼyar ƙabilar, inji Shettima

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya bayar da kariya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu akan zarge-zargen cewa yana ɗaya daga cikin masu ƙiyayya ga ƙabilar Igbo, yana mai cewa da Shugaban ba zai bar ɗansa Seyi ya auri inyamura ba idan ba ya son ƙabilar.

Shettima ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, yayin taron yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a birnin Awkan Jihar Anambara na Solu/Tinubu, inda ya buƙaci ‘yan Kudu maso Gabas da su sake zaɓar Shugaba Tinubu a karo na biyu. “Shugaba Tinubu aboki ne ga Igbo. Ɗansa Seyi yana auren wadda ta fito daga Igbo. Idan har ya tsani Igbo, da ba zai bar ɗansa ya auri ‘yarsu ba,” inji shi.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ƙara da cewa, “Don haka dukkan mu al’umma ɗaya ne. Igbo mutane ne masu muhimmanci wajen saita al’amuran Nijeriya.”

Seyi Tinubu yana auran Layal Jade Tinubu, wadda ‘yar kasuwa ce ta Nijeriya da ke zama a Lebanon kuma mai taimakon al’umma, sannan mahaifanta ‘yan Jihar Anambara ne. Ma’auratan sun yi aure ne a watan Agustan 2016, wanda aka gudanar da bikinsa a Legas da kuma Villa Erba da ke Lake Como a ƙasar Italiya. An yi bikin auren ne a ranar 10 ga Agusta, 2016.

Tuni dai Shettima ya tabbatar wa al’ummar shiyyar Kudu maso Gabas cewa daga wajensu za a samar da shugaban Nijeriya na gaba idan mulki ya koma kudu. Wannan gangami ɓangare ne na ƙoƙarin jam’iyyar APC wajen ƙarfafa goyon bayan siyasarta a Kudu maso Gabas gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

By Babaji

Leave a Reply