Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 14.06 a Nijeriya – NBS

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Aididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta ragu zuwa kashi 14.06 cikin 100 a watan Oktoban 2026, idan aka kwatanta da kashi 14.63 cikin 100 da aka samu a watan Satumban wannan shekara.

A cikin rahotonta kan ma’aunin sauyin farashin kayayyaki da masu amfani ke saya (CPI), wanda ta fitar a ranar Litinin, hukumar ta ce an samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki da maki 0.43 cikin 100 a watan Oktoba, idan aka kwatanta da watan Satumba.

Sai dai hukumar ta bayyana cewa idan aka auna sauyin farashin kayayyaki daga wata zuwa wata, an samu hauhawar kashi 0.43 cikin 100 a watan Oktoba, wanda ya haura da maki 0.38 idan aka kwatanta da kashi 0.06 da aka samu a watan Satumba. Hukumar ta ce, wannan na nufin cewa duk da raguwar hauhawar farashin kayayyaki idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, saurin tashin matsakaicin farashin kayayyaki a watan Oktoba ya fi wanda aka samu a watan Satumba.

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa ta kuma bayyana cewa hauhawar farashin kayan abinci a Nijeriya ta kai kashi 19.13 cikin 100 a watan Oktoban 2026, idan aka kwatanta da makamancin watan a shekarar da ta gabata.

Wannan adadi ya nuna raguwar hauhawar farashin kayan abinci idan aka kwatanta da kashi 19.59 cikin 100 da aka samu a watan Satumban 2026. Sai dai hukumar ta ce adadin watan Oktoban ya fi kashi 16.30 cikin 100 da aka samu a makamancin watan shekarar 2025. A cewar hukumar, idan aka kwatanta sauyin farashin kayan abinci daga wata zuwa wata, an samu raguwar kashi 0.75 cikin 100 a watan Oktoba, wanda ke nuna sauyi mai maki 0.80 idan aka kwatanta da raguwar kashi 1.55 da aka samu a watan Satumba.

Hukumar ta danganta wannan sauyin da yadda farashin wasu muhimman kayan abinci ya canja, ciki har da man girki, kifin gwangwani na Titus, koren wake da ake sayarwa a ƙunshe, kifin makarel, kifin croaker, shinkafa ta gida, kifin tarwaɗa, kayan ciki na saniya, man ja da kuma gero da ake sayarwa.

Haka kuma, hukumar ta bayyana cewa matsakaicin hauhawar farashin kayan abinci na shekara-shekara, idan aka yi la’akari da watanni 12 da suka ƙare a Oktoban 2026, ya kai kashi 15.98 cikin 100.

Wannan adadi ya yi ƙasa da na makamancin lokacin shekarar 2025 da maki 10.49, domin a lokacin matsakaicin hauhawar ya kai kashi 26.47 cikin 100. Hukumar ta ce idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, Jihar Ondo ce ta fi fuskantar hauhawar farashin kayan abinci, inda aka samu kashi 31.74 cikin 100. Jihar Legas ce ta biyo baya da kashi 31.43, yayin da Jihar Imo ta zo ta uku da kashi 29.75 cikin 100.

A ɓangaren jihohin da suka samu mafi ƙarancin hauhawar farashin kayan abinci idan aka kwatanta da bara, Jihar Nasarawa ce ta kasance a kan gaba da kashi 3.70 cikin 100, sai Bayelsa da kashi 7.11, sannan Kano da kashi 7.13. Haka kuma, idan aka kwatanta sauyin farashin kayan abinci daga wata zuwa wata, Jihar Yobe ce ta fi fuskantar hauhawar farashin, inda aka samu kashi 18.41 cikin 100. Jihar Kebbi ta biyo baya da kashi 16.45, yayin da Jihar Borno ta samu kashi 13.96 cikin 100.

Sai dai a wasu jihohin an samu raguwar farashin kayan abinci a wannan ma’auni, inda Legas ta samu raguwar kashi 5.93 cikin 100, Filato kashi 5.83, sannan Binuwe kashi 5.49 cikin 100.

By ukarofi

Leave a Reply