Legas: Gobara ta laƙume shaguna da dama a Kasuwar Ikotun

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata gobara da ta tashi a Kasuwar Ikotun da ke kusa da yankin Synagogue, a Jihar Legas, ta ƙone shaguna da dama tare da lalata wasu gine-gine.

Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta tashi ne da safiyar Lahadi, inda ta haddasa babbar asara ga ’yan kasuwa sakamakon lalacewar shaguna da wasu gine-gine da ke cikin kasuwar. Hukumar Kashe Gobara da Ceto ta Jihar Legas ta tabbatar da faruwar lamarin a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na ɗ, inda ta ce ta samu kiran neman agajin gaggawa da misalin ƙarfe 10:24 na safe.

Hukumar ta bayyana cewa, jami’an kashe gobara daga tashoshinta na Ejigbo da Isolo sun isa wurin da misalin ƙarfe 10:36 na safe, wato bayan mintuna 12 da samun kiran, inda nan take suka fara ƙoƙarin shawo kan gobarar. Hotunan bidiyo da Hukumar Kashe Gobara ta fitar sun nuna irin barnar da gobarar ta yi, inda aka ga shaguna da dama sun ƙone ƙurmus, rufin wasu gine-gine na ƙarfe ya rufta, yayin da tarkacen siminti da sauran kayan gini suka watse a sassan kasuwar da gobarar ta shafa.

Haka kuma, hayaƙi mai yawa ya turnuƙe yankin, yayin da jami’an kashe gobara ke zagayawa cikin wuraren da abin ya shafa domin kashe sauran harshen wutar da kuma hana ta bazuwa zuwa wasu sassan kasuwar. A lokacin haɗa wannan rahoto, hukumar ba ta gano ko bayyana musabbabin tashin gobarar ba.

A wani saƙo na daban, Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Legas (LASTMA) ta tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa a gobarar. Hukumar ta ce jami’an agajin gaggawa na ci gaba da aikin kashe wutar baki ɗaya. “Ya zuwa yanzu, babu wanda aka tabbatar da mutuwarsa,” inji hukumar, inda ta ƙara da cewa, “ana ci gaba da haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tabbatar da cewa an kashe gobarar gaba ɗaya.”

Hukumar LASTMA ta kuma sanar da rufe dukkan layin hanyar da ke shiga yankin Synagogue sakamakon gobarar. Ta ce an samar da tsarin bai wa ababen hawa damar amfani da layin da ke kishiyar hanya domin rage cunkoson ababen hawa a hanyar da lamarin ya shafa, yayin da jami’an agajin gaggawa ke ci gaba da aikinsu. Hukumar ta shawarci masu ababen hawa da su lura da sabon tsarin zirga-zirgar, tare da taka-tsantsan yayin tunkarar yankin.

A lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomi ba su tantance yawan asarar kuɗin da ’yan kasuwar suka yi ba, haka kuma ba a bayyana musabbabin tashin gobarar a hukumance ba.

By ukarofi

Leave a Reply