Kano: Gobara ta lalata sama da shaguna 100 a kasuwar kifi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata gobara a kasuwar kifi da ke kan hanyar zuwa Zariya a Jihar Kano, ta lalata sama da shaguna guda 100, lamarin da ya jefa ƙananan ‘yan kasuwa cikin asara da adadinta ya kai biliyoyin nairori.

Gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar Lahadi, a kusa da tashar motar Kano Line, wadda ta bazu a sassan kasuwar da tarwatsa shaguna, maɗaukai da wasu kayayyaki. Wasu rahotanni sun nuna cewa aƙalla za a samu shaguna 150 da maɗaukai 200 da gobarar ta shafa, inda wasu ‘yan kasuwar suka yi asarar miliyoyin naira a sanadiyyar haka.

Wani ɗan kasuwar da iftila’in ya shafa mai suna Usman Sani, ya bayyana yadda gobarar ta bazu a sassan kasuwar, inda ta lalata shaguna da kayayyaki kafin ‘yan kasuwar su yi ƙoƙarin kwashe dukiyoyinsu.

Wani Musa Inuwa, wanda shi ma ɗan kasuwar ne ya bayyana al’amarin a matsayin babban iftila’i ga waɗanda suka dogara da kasuwar wajen gudanar da lamuran rayuwarsu ta yau da kullum. “Da dama daga cikinmu mun dogara ne da wannan sana’a wajen ciyar da iyalanmu. Mun yi asarar kayayyaki da jarinmu…Mu na kira ga gwamnati da ta kawo mana ɗauki,” inji shi.

Waɗanda iftila’in ya rutsa da su sun roƙi Gwamnatin Jihar Kano da hukumomi masu ruwa da tsaki da su kai musu agajin gaggawa don farfaɗowa daga halin da suka samu kansu a ciki. Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, ba a bayyana ainihin dalilin da ya haddasa aukuwar gobarar ba duk da jami’an hukumar kashe gobara sun kai agajin gaggawa a kai.

By Babaji

Leave a Reply