Dambarwar Sarkin Daura: Gwamnatin Katsina ta yi gum yayin da masarautar ta fara binciken bidiyo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Masarautar Daura a Jihar Katsina ta ce ta fara gudanar da nazari akan wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta wanda a ciki wata ‘yar yawon buɗe ta ƙasar Poland, Mirka Czee, ta zargi Sarkin Daura, Mai Martaba Faruk Umar Faruk da cin zarafinta ta hanyar yunƙurin lalata da ita a fadarsa, yayin da Gwamnatin Jihar Katsina zuwa yanzu ba ta fitar da wani saƙo ba a hukumance akan zargin.

Rahotanni sun ce, majalisar ta bakin Kakakinta, Ibrahim Daura, ta ce tana nazari akan ɗaukar domin gano sahihancinta da kuma ko an yi amfani da fasahar AI ne wajen shirya ta. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Al’ada da Yawon Buɗe Ido na jihar, Dakta Bala Zango, ya ce bai kai ga ganin bidiyon ba, amma zai samo ya kalla kafin ya bayar da amsa akan tambayoyin da aka masa kan zargin.

Sarkin Labaran Daura, Ibrahim Murtala Daura ne ya sanar da wannan ci-gaba, inda ya ce a yau Litinin ne majalisar masarautar ta samu labarin yaɗuwar bidiyon a Soshiyal Mediya don haka za ta fitar da bayanai a kai da zarar ta kammala bincikenta a kai. Matsayar majalisar ta biyo bayan da Czee, wadda ke amfani da Instagram @beduinqa, ta jaddada zarginta a wallafe-wallafe daban-daban, inda ta yanke bayyana wa al’umma da faɗar yadda hakan ya yi tasirin shauƙi akanta.

Matar, wadda aka haifa a kasar Czech Republic, ta ce ta yawata a sassan Nijeriya ciki har da Oron, Calabar, Ibadan, Benin City, Lagos, Abeokuta, Osogbo, Ilorin, Abuja, Jos, Bauchi, Dutse, Kano, Zaria, Katsina da kuma Daura. A cewarta, tana tafiye-tafiyen nata ne a motocin ‘yan kasuwa kuma tana tattaunawa da mazauna domin gane yadda al’adu da bambance-bambancen Nijeriya suke, inda ta ƙara da cewa ta haɗu da mutanen kirki masu taimako da karrama mutane.

Sannan, ta ce ta gana da wasu sarakuna a Nijeriya da bayyana hakan a matsayin abin da aka yi bisa girmamawa. Kazalika, ta yi zargin cewa a lokacin da ta je fadar ta Daura, an nuna mata ababen tarihi a wasu wurare ciki har da kai ta wajen da ta haye kan doki da nufin nishaɗi. A cewarta, daga bisani an mayar da ita wajen Sarkin, saidai an bar ta ita kaɗai a wani babban ɗaki daga ita sai sarkin.

Ta yi zargin cewa, sarkin ya buƙaci da ta zauna a kusa da shi akan wata kujera, inda ya riƙe hannunta ya fara wasa da shi, lamarin da ya sa ta fara jin ta a halin takura. Czee ta ce, a lokacin ne ta sauke tabaranta mai ɗauke da kyamara da sanya shi a halin naɗar abin da ke faruwa a daidai lokacin da ta yi ƙoƙarin jan hankalinsa don cigaba da hirar tsakaninsu.

Matar ta kuma yi zargin cewa sarkin daga bisani sai ya rungume ta ya kuma sumbace ta a kumatu yayin da suka miƙe tsaye kafin ya taɓa mata mama ba tare da amincewarta ba. Ta bayyana cewa hakan ya girgiza ta, inda ta cigaba da faɗa masa cewa ya daina taɓa ta.

By Babaji

Leave a Reply