Mu guji mayar da tarukan siyasa dandalin zubar da jini

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Yayin da ‘yan Nijeriya ke shirye-shiryen tafiya zuwa rumfunan zaɓe don zaɓar shugabannin da za su jagoranci al’amuransu a matakai daban-daban na gwamnatin dimokuraɗiyya, yana da muhimmanci mu fahimci cewa, wuraren tarukan gangamin yaƙin neman zaɓe ba filin goge raini, far wa abokan adawa, ko zubar da jini ba ne. 

Na fara buɗe rubutuna na wannan mako ne da waɗannan kalamai domin su zama manuniya ga ’yan uwana matasa ’yan Nijeriya su sani cewa siyasa ba gaba ba ce! ɗaukar makamai da nufin tarwatsa taron masu gangamin yaƙin neman zaɓe don a hana su ’yancinsu na bayyana goyon bayansu ga ɗan takarar da suke so, da neman goyon bayan jama’a, abu ne da ya saɓawa doka, da kuma tsarin dimokuraɗiyya.

Ana samun rahotanni a kafafen watsa labarai da ke bayyana yadda wasu ɓatagarin matasa ke kai hare-hare a wuraren tarukan yaƙin neman zaɓe, tare da lalata allunan tallata ’yan takara, lalata motocin yawon kamfen, raunata magoya bayan ɗan takara, har ma da jikkata wasu da makamai. Dawowar irin wannan tsohuwar al’ada ta bangar siyasa da far wa tarukan jam’iyyar adawa da magoya bayansu, babban abin takaici ne da ke haifar da koma baya ga tsarin dimokraɗiyya. Sannan harwayau hakan na ƙara sanya tsoro da fargaba a zukatan ’yan Nijeriya da har yanzu ke ganin siyasar mu ta gurɓace da faɗace-faɗace, da cutar da juna, don razana abokan adawa. 

Ya kamata matasa su fahimci cewa tashin hankali ba zai taimaka mana lashe zaɓe ba; sai dai ya ma ƙara cutar da rayukan jama’ar da basu ji ba, ba su gani ba, da kuma lalata kima da ingancin dimukraɗiyyar da muke iƙirarin karewa.

Wasu rahotanni na baya-bayan nan sun nuna cewa, an samu labarin hare-haren da ake zargin wasu ‘yan tada zaune tsaye ne suka kai kan tarukan siyasa da masu goyon bayan jam’iyyun adawa. Misali, a Jihar Legas, an ce wasu matasa masu ɗauke da makamai sun tarwatsa wani taron ’yan siyasa da jam’iyyar adawa ta NDC ta shirya a yankin Oregun da ke Ikeja; wanda hakan ya bar wasu masu goyon bayan jam’iyyar cikin jini da jikkata, yayin da kuma aka lalata wasu motoci.

Haka ma, a Jihar Gombe, an samu rahoton wasu ‘yan daba sun ƙona tayoyi, tare da toshe hanya, sannan suka farfasa gilasan wasu motoci da kuma jikkata mutanen da ke ciki, yayin da ayarin motocin wani ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP suka ke wucewa. A Jihar Katsina, ‘yan sanda sun ce an kai hari kan wasu magoya bayan jam’iyyar APC yayin da suke tafiya zuwa taron yaƙin neman zaɓe; har an jefe su da duwatsu, an ƙona allunan tallata ’yan takara, har ma da ƙona wata mota. Mun ji irin haka a Jos, Kano, da Kebbi, yayin da shafukan sada zumunta ke cigaba da yaɗa irin waɗannan bidiyoyi, na yadda gangamin yaƙin neman zaɓe ke neman zama tarkon mutuwa, ko sansanin zubar da jini.

Waɗannan ba rahotanni ne na ƙanzon kurege ba, abubuwa da suke faruwa akan idanunmu a garuruwan mu, wani lokaci ma har a gaban jami’an tsaro. ƙungiyoyi masu aikin sa’ido kan harkokin siyasa a Nijeriya, sun bayar da rahoton cewa, fiye da hare-hare 30 kan masu yaƙin neman zaɓe, ‘yan takara, masu goya musu baya, da ma motocin kamfen, da tarukan siyasa, duk sun fara faruwa ne daga lokacin da Hukumar Zaɓe ta INEC ta sanar da fara yaƙin neman zaɓe a watan Agusta, inda fiye da mutum 10 suka mutu.

A wani rahoton makamancin wannan kuma an bayyana cewa, a cikin hare-hare 70 da aka kai wa masu yaƙin neman zaɓe a jihohi 19 har da Babban Birnin Tarayya Abuja tsakanin Janairu da Oktoba, inda aka samu asarar rayuka har mutane 27 suka mutu a cikin hare-hare 20.

A bayan kowanne allon talla da aka lalata, akwai yiwuwar wani matashi wanda zai iya fuskantar kamu, jikkata ko mutuwa. A bayan kowacce motar kamfen da aka kai wa hari, akwai iyalai da za su iya rasa mai tallafa musu, yaro ko aboki. A yayin hare-haren da aka kai kan wasu masu goyon bayan jam’iyyar NDC a Jihar Delta, an ce wani mutum ɗaya ya mutu, sannan wasu biyar suka samu jikkata; a wani labarin ma, an ce an lalata fiye da motoci 30, sannan fiye da masu goyon baya 10 suka jikkata.

Tashin hankalin siyasa ba abu ne mai kyau ba. Idan an tuna a Jihar Kano a sakamakon irin wannan yamutsi na siyasa ne ya yi sanadiyyar kashe tsohon fitaccen ɗan siyasar nan Dr Bala Muhammad, tsohon mijin ýar siyasar nan kuma ’yar gwagwamaya Hajiya Naja’atu Muhammad. Lamari ne da idan ba Allah ya kiyaye ba yana iya wuce kan waɗanda aka kai musu hari kai tsaye har da iyalansu da ’yan uwansu. 

Wannan lamari yana matuƙar tsoratar da masu zaɓe daga zuwa wuraren tarukan siyasa, ko zuwa rumfanan zaɓe a ranar zaɓe, yana kuma hana ’yan takara masu daraja tsayawa takara, yana kawo rabuwar kai a tsakanin al’umma saboda bambancin jam’iyya. Sannan yana ba hukumomi dalilan ɗaukar wasu matakai na taƙaita ayyukan ’yan siyasa ko ƙara takura ýan adawa.

Ya kamata mu ƙara fahimtar cewa lokacin da ake amfani da matasa a matsayin ‘yan bangar siyasa, ya wuce. Bai kamata mu cigaba da biyewa wasu masu son zuciya da baragurbin ’yan siyasa suna amfani da mu wajen cimma manufofinsu na siyasa ba, wanda a ƙarshe galibi suna watsi da mu ne bayan burinsu ya cika! Idan ba mu yi sa’a ba kuma mu fuskanci kamu, ɗauri, tuhuma ko ma kisa, yayin da ‘yan siyasar da muka yi wa aiki suke ɗauke kansu daga abubuwan da suka faru da mu.

Amma babu ɗan siyasa da darajar sa ta cancanci sadaukar da taka rayuwar, kuma babu wani ɗan siyasar da yake ganin sadaukarwarka a matsayin abin girmamawa ce a wajensa. Duk ɗan takarar da yake ganin ya cancanta a zaɓe shi, ba ya buƙatar amfani da ’yan daba ko ’yan ta’adda don ya samu galaba a kan l abokan hamayyarsa. Halayensa da ƙwarewarsa, da iya isa ga masu zaɓe su ne za su taimaka masa ya samu rinjaye a wajen zaɓe, ba ya matasa su ɗauki makami, don su taimaka masa ya samu mulki. Matashi mai natsuwa da aiki da hankali, yana nuna goyon bayansa ne da kare ɗan takararsa da hujjoji masu ƙarfi, bayyana ra’ayinsa cikin ’yanci da natsuwa, neman goyon bayan masu zaɓe cikin lalama da gamsassun bayanai, da amfani da hanyoyi na lumana wajen neman yardar jama’a, ba ta hanyar amfani da tashin hankali, amfani da makami, duwatsu, bindigogi ko ƙone-ƙone ba.

Lalata allon tallata abokin hamayya ba zai sa ɗan takararka ya samu nasara ba. Toshe hanya da tayar da tarzoma, ba zai inganta tattalin arzikin mu ba. Kai hari kan masu goyon bayan jam’iyyar abokan hamayya ba zai samar mana da ayyuka yi ba, ba zai gyara mana makarantu ba, ba zai magance mana matsalar tsaro, ko kuma inganta kiwon lafiyarmu ba. Yana ƙara mana ƙiyayyar juna ne kawai, sannan yana mai da ranar zaɓe ta zama ranar tsoro da fargaba, ba ranar ’yanci da aminci ga kowa ba.

By ukarofi

Leave a Reply