Yadda kyamara ta nuna wata ma’aikaciyar jinya na faɗa da mara lafiya a gadon asibiti

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani faifan bidiyo da ya nuna wata ma’aikaciyar jinya a Nijeriya tana kai wa wani mara lafiya da ake jinya hari a asibitin gwamnati ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.

Bidiyon ya nuna ma’aikaciyar jinyar tana nufar wani mutum da ba shi da lafiya, wanda ke kwance a gadon asibiti, sannan ta shiga fafatawa da shi ta hanyar amfani da ƙarfi.

A wani lokaci, an ga wani mutum da wata mata suna ƙoƙarin riƙe ma’aikaciyar jinyar domin hana ta ci gaba da kai wa mara lafiyar hari, yayin da shi kuma yake kwance a gadon.

Daga tattaunawar da aka ji a cikin bidiyon, an ce saɓanin ya samo asali ne bayan mara lafiyar ya koka cewa hasken asibitin ya yi yawa, sannan ya nemi a yi amfani da audugar da ke kusa da gadonsa a matsayin labule domin rage hasken.

Sai dai ana zargin ma’aikaciyar jinyar ta ƙi amincewa da buƙatar, tana mai cewa irin wannan tsari na yiwuwa ne a asibitin masu zaman kansu kawai, ba a asibitin gwamnati ba. An kuma ji tana nuna cewa ba ta son ci gaba da jinyarsa.

Lamarin ya janyo damuwa da martani daga masu amfani da kafafen sada zumunta, inda da dama suka yi tambaya kan yadda ma’aikaciyar lafiya za ta shiga faɗa da mutumin da aka kwantar a asibiti domin jinya.

Bidiyon ya kuma sake tayar da muhawara kan walwalar marasa lafiya, ɗabi’ar ma’aikatan lafiya da kuma nauyin da ke kansu na tabbatar da cewa ana kula da marasa lafiya a cikin yanayi mai aminci.

A halin da ake ciki, wasu sun yi kira ga shugabancin asibitin da hukumomin lafiya da su gudanar da bincike kan lamarin, su gano abin da ya jawo saɓanin, sannan su ɗauki matakin da ya dace idan an ga buƙatar hakan.

Martanin masu amfani da kafafen sada zumunta

Bayan yaɗuwar bidiyon, mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu kan abin da ya faru.

Wani mai amfani da kafar sada zumunta mai suna allshadesof_best ya ce: “Idan ba za ka iya sarrafa kanka ba, ba ka da aikin yi a fannin lafiya.”

Theamakaanthonybrand ya ce yana ganin ya kamata a tattauna kan rashin ƙwarewa da ɗabi’a da ake zargin wasu ma’aikatan jinya a asibitocin Nijeriya suna nunawa.

Ya ba da labarin yadda mahaifiyarsa ta taɓa kwanciya a asibiti, inda ya ce wasu ma’aikatan jinya ba su kula da ita yadda ya kamata ba. A cewarsa, wata rana mahaifiyarsa tana karɓar ruwan magani ta hanyar allura, amma ruwan ya ƙare da misalin ƙarfe biyu na dare, jini kuma ya fara komawa cikin bututun.

Ya ce sun danna ƙarar neman taimakon ma’aikatan jinya sau da dama amma babu wanda ya zo. Daga baya, ya fita daga ginin da mahaifiyarsa take kwance zuwa wani gini domin neman ma’aikatan jinya, inda ya same su suna barci a wurin karɓar baƙi.

Ya ce duk da ya je ya kira su, sai da suka ɗauki wasu mintuna 15 kafin su zo. Ya kuma ce a wani lokaci da suka nemi maganin dare na mahaifiyarsa, sun jira kusan awa ɗaya kafin wata ma’aikaciyar jinya ta zo, amma maimakon ta ba ta maganin da kanta, sai ta miƙa wa shi ta ce, “Ka ba ta.”

Ya ce ya tambayi ma’aikaciyar jinyar ko shi ne zai ba mara lafiyar magani, yana mai cewa bai ji daɗin yadda ta miƙa masa maganin ba tare da sanin ko shi wanene ko kuma abin da yake niyyar yi ba.

Ya ƙara da cewa ma’aikatan jinyar ba su taimaka sosai wajen wanke mahaifiyarsa, tsaftace ta ko biyan wasu buƙatunta na yau da kullum ba, har ta kai ga shi da iyalinsa suke yin yawancin ayyukan da ya kamata ma’aikatan asibitin su yi.

Ya ce sun biya fiye da naira 500,000 na kwanaki huɗu a asibitin, amma mahaifiyarsa ta koma gida ba tare da ta warke ba. Sai dai ya jaddada cewa ba dukkan ma’aikatan jinya ne suke nuna irin wannan ɗabi’a ba, yana mai cewa akwai masu ƙwazo da tausayi.

A cewarsa, ya kamata a gyara tsarin kula da lafiya a Nijeriya, domin ma’aikatan lafiya suna kula da rayukan mutane, ba aikin da za a yi ba tare da kulawa da nauyin da ke kansa ba.

Okonlagos ya ce: “Sanin lokacin da za ka tsaya kan ra’ayinka da kuma lokacin da ya kamata ka ja da baya abu ne mai muhimmanci. A yanzu, da kanta ta taimaka wajen samar da hujjar da za a iya amfani da ita wajen soke lasisin aikin jinyarta.”

Ya kuma soki waɗanda ke kare ta, yana mai cewa babu hujjar da za ta sa ma’aikaciyar jinya ta dinga dukan mara lafiya da ke kwance a gadon asibiti.

Wani mai sharhi a shafin ya ce ma’aikaciyar jinyar bai kamata ta ci gaba da aiki a asibiti ba, yana mai kira da a sallame ta daga aiki nan take.

By ukarofi

Leave a Reply