Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Shugaban ƙungiyar Masu Karɓar Fansho ta ƙasa, babban ɗan ƙasa Shuaibu Musa Jibrin, ya bayyana cewa Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gaji bashin kuɗin fanshon Kano naira biliyan 48 da miliyan 6.
Ya ce gwamnan ya yi alƙawarin cewa idan aka zaɓe shi a matsayin gwamnan Kano, zai biya ’yan fansho haƙƙoƙinsu. A cewarsa, tun bayan zaɓen da aka yi masa a shekarar 2023, gwamnan ya biya kuɗi har naira biliyan 37, wanda ya kai sama da kashi 90 cikin 100 na bashin sallamar aiki da ’yan fanshon Kano suka biyo tun daga gwamnatocin baya.
Shuaibu Musa Jibrin ya bayyana hakan ne a wajen bikin ƙaddamar da rabon kuɗin fansho karo na bakwai, wanda gwamnan ya jagoranta a ɗakin taro na gidan gwamnatin Kano ranar Litinin ɗin da ta gabata.
Alhaji Shuaibu ya ƙara da cewa gwamnan ya biya naira biliyan 6 a karo na farko, biliyan 5 a karo na biyu, biliyan 5 a karo na uku, biliyan 6 a karo na huɗu, biliyan 5 a karo na biyar, biliyan 5 a karo na shida da kuma biliyan 5 a karo na bakwai. A cewarsa, jimillar kuɗin da aka biya ta kai naira biliyan 37 cikin shekaru uku na gwamnatin Abba.
Ya ce gwamnan ya yi alƙawarin ci gaba da biyan kuɗin duk wata har zuwa watan Afrilu na 2027, da yardar Allah. Saboda haka, Musa Jibrin ya ce suna yabawa gwamnan bisa cika alƙawarinsa kuma suna tare da shi.
Shi ma, Shugaban Hukumar Fansho ta Jihar Kano, Hon. Habu Muhammad Fagge, ya bayyana cewa nasarorin da hukumar ke samu sun samo asali ne daga cika alƙawarin da Gwamna Abba ya yi.
Ya buƙaci ’yan fansho da sauran al’ummar Kano su ci gaba da bai wa gwamnati haɗin kai da addu’ar ci gaba, zaman lafiya, arziki, tsaro da kwanciyar hankali a Kano da ƙasa baki ɗaya.
