A karon farko Islamiyyar Rabi’u Adamu ta yi saukar yaye ɗalibai 19 a Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe 

Makarantar Rabi’u Adamu Memorial Islamic School da ke unguwar G.R.A a Gombe ta shiga tarihin ci gaban ilimin addinin Musulunci, bayan da ta gudanar da bikin saukar Alƙur’ani na farko tun bayan kafuwarta, inda ɗalibai 19 suka kammala karatun Alƙur’ani gaba ɗaya.

Makarantar, wadda ke ƙarƙashin kulawar Imam Abdullateef Sheikh Modibbo Tukur (R.T.A.), ta fara ne da ɗalibai takwas kacal, amma yanzu ta kai sama da ɗalibai 300, abin da ke nuna irin karɓuwa da amincewar da ta samu daga al’ummar Musulmi a jihar Gombe.

A yayin bikin, masana da malamai daga jami’o’i da cibiyoyin ilimi sun bayyana muhimmancin tabbatar da ingantaccen koyar da Alƙur’ani ga yara tun ƙuruciya. Malam Muhammad Tukur Abdullahi daga Jami’ar Tarayya ta Kashere ya yi bayani kan ma’anar Waƙafi da rawar da yake takawa wajen daidaita karatun Alƙur’ani, tare da jan kunnen ɗalibai da malamai su riƙa bin ƙa’idoji domin tabbatar da sahihin karatu.

Shugaban Ciɓil Society GONET, Ibrahim Yusuf 3000, ya bayyana Alƙur’ani a matsayin gadon da ya fi kowace dukiya daraja ga yara, yana mai yabawa makarantar bisa gina tubalin tarbiyya da ilimin Musulunci ga ƙananan yara.

Haka nan Farfesa Shamsuddeen Ilyas, Daraktan Cibiyar Binciken Addinin Musulunci ta Jami’ar Gombe, da sauran manyan baƙi kamar Farfesa Sani Manga, Alhaji Imamu Jauro Dan-Lawan da Alhaji Ahmadu Shuaibu Gara, sun nuna farin ciki tare da kira ga gwamnati da masu hannu da shuni su tallafa da kayan koyarwa domin ƙara inganta tsarin ilimi a makarantar.

Duk da wannan cigaba, shugaban makarantar Imam Abdullateef Modibbo Tukur ya bayyana cewa suna fuskantar ƙarancin kujeru da kayayyakin karatu, inda ya roƙi jama’a da shugabanni su ci gaba da bayar da gudunmawa domin cigaba da raya makarantar.

Sheikh Modibbo Isah Shongo ya tunatar da iyaye da dalibai bukatar ganin darasin Alƙur’ani ya bayyana a rayuwa ta yau da kullum, yayin da Khalifan Sheikh Modibbo Tukur, Sheikh Mahmoud Modibbo Tukur, ya jinjinawa malamai, iyaye da duk masu hannu da shuni kan wannan nasara.

Daga cikin dalibai 19 da suka sauke Alƙur’ani, maza biyar ne yayin da mata suka kai 14, lamarin da ya sa bikin ya kasance abin tarihi ga makarantar da al’ummar Musulmi a Gombe baki ɗaya.

By ukarofi