A shirye mu ke domin cigaba da bibiyar shari’ar Walida – Gwamna Namadi

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da bin shari’ar sace Walida Abdulhadi har zuwa ƙarshen ta, domin tabbatar da adalci da kuma haɗa ta da iyalanta nan ba da jimawa ba. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar ga manema labarai.

Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da ya gana da iyayen Walida tare da lauyansu a fadar gwamnati da ke Dutse.

Gwamna Namadi ya shaida musu halin da Walida ke ciki a yanzu, yana mai jaddada ƙudirin gwamnati na tabbatar da cikakken jinyarta, komawarta makaranta da kuma kula da jin daɗin ta gaba ɗaya.

Ya kuma ce Walida na karɓar kulawa a wani asibiti da gwamnatin jihar ke ɗaukar nauyinta, kuma za a mayar da ita ga iyalanta bayan kammala duba lafiyar ta. Haka kuma, gwamnati ta tura ƙwararrun ma’aikatan jin ƙai domin ba ta da ‘yarta tallafin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa da zamantakewa, tare da tabbatar da cewa za a mayar da ita makaranta.

Gwamnan ya ƙara da cewa duk wanda aka samu da hannu a lamarin za a gurfanar da shi a gaban kuliya domin tabbatar da adalci.

By ukarofi