Sauye-sauyen tattalin arziki na Tinubu sun fara haifar da ɗa mai ido – Idris

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Ministan yaɗa labarai da wayar da kai na ƙasa, Mohammed Idris, ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa sun fara nuna sakamako a fili. Idris ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin ministar masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Jumoke Oduwole, wadda ta kai masa ziyarar girmamawa a ma’aikatar sa.

Idris ya ce a karon farko cikin shekaru 13, ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje na Najeriya ya haura dala biliyan 50. Ya kuma ƙara da cewa an cire Najeriya daga jerin ƙasashen da ke cikin “grey list” na Financial Action Task Force, lamarin da ke aika saƙo mai kyau ga masu zuba jari a duniya cewa Najeriya a shirye take domin halastattun harkokin kasuwanci.

Ya ƙara da cewa ma’aikatar yaɗa labarai za ta ci gaba da tallata manufofi da shirye-shiryen gwamnatin tarayya, musamman waɗanda ke nufin ƙarfafa tattalin arziki da jawo zuba jari.

A nata ɓangaren, Oduwole ta ce ziyarar ta su na da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatun biyu domin tallata manufofin gwamnati, yayin da Najeriya ke ƙoƙarin bunƙasa masana’antu, ƙara kasuwanci da kuma yawan kayayyakin da ake fitarwa zuwa ƙasashen waje ba tare da dogaro da man fetur kaɗai ba.

By ukarofi