Abdulsamad Rabiu ya shiga sahun mutane huɗu mafiya arziki a Afirka

Daga AMINA YUSUF ALI

A yanzu haka dai sakamakon rahoton jaridar tattalin arziki ta Forbes ya bayyana AbdusSamad Isyaku Rabiu a matsayin mutum na 4 a jerin mutane mafiya arziki a Afirka. Wato ya ture Attajirin nan na ƙasar Masar, Nassef Sawiris, wanda a da shi ne mutum na huɗu mafi arziki a Duniya.

Da ma a watannin da ba su wuce biyu baya ba, AbdusSamad Rabi’u wanda shi ne mallakinta rukunin kamfanonin BUA ya samu muƙamin mutum na biyu mafi arziki a Nijeriya bayan ya kere Attajirin da yake gabansa a arziki wato, Mike Adenuga.

Jaridar Forbes ita ta ba da wannan rahoto.

A yanzu haka dai arzikin Abdussamad (BUA) ya ƙaru da sama da Dalar Amurka biliyan $2.4 a shekarar da ta gabata, wato ƙarfin arzikinsa ya ɗaga daga Dalar Amurka biliyan $4.9 zuwa biliyan $7.6 a dai-dai lokacin da ake rubuta wannan rahoton.

Wannan hauhawar dukiyar tasa a cikin gajeren lokaci ita ta mai da shi ya zama mutum na huɗu mafi arziki a Duniya.

Wato bayan Biloniya Ɗangote, wanda shi ne na farko a arziki a Afirka gabaɗaya, da wasu biloniyoyi guda biyu daga Afirka ta Kudu wato, Johann Rupert da Nicky Oppenheimer.

Ya samu muƙamin bayan ya kere Biloniya Nassef Sawiris, na ƙasar Masar wanda a yanzu ƙarfin arzikinsa yake Dalar Amurka biliyan $7.3, yayin da shi kuma BUA yake a Dalar Amurka biliyan $7.6.

Kafin haka, Sawiri wanda yawanci dukiyarsa ta samu ne daga kamfanoni da da suke a Adidas da OCI N.V.l., ya kasance shi ne mutum mafi arziki a duk faɗin Afirka ta Arewa da duniyar Larabawa gabaɗaya.

Abdussamad Rabi’u ya kasance yana samun kuɗinsa ta hanyar rukunin kamfanoninsa wato BUA Group, wanda ya kasance kamfanin da ya fi kowanne saurin bunƙasa a nahiyar Afirka.

A halin yanzu kuma shi ne mutum mafi arziki na huɗu a Afirka, kuma mafi arziki na biyu a Nijeriya.