Abin da ya sa Tinubu bai halarci buɗe ayyukan Legas ba – Mataimaki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa akan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan al’umma, Sunday Dare ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu bai samu halartar taron buɗe ayyuka a Legas ba ne saboda ba’asin tsaro da ke gudana.

A wata hira da gidan talabijin na Channels, Dare ya ce Shugaba Tinubu ya fifita ci-gaban tsaron ƙasa akan taron da kuka wasu muhimman ayyukan da suka shafi ƙasa.

Sunday Dare ya kuma ce shugaban yana aiki tare da jagororin tsaro kafaɗa-da-kafaɗa wajen karɓar rahotanni ci-gaba a fannin musamman bisa la’akari da hare-haren da suke faruwa a sassan ƙasar.

A cewarsa, Tinubu ya mayar da hankali ne akan tuntuɓa da tattauna hanyoyin da za bi wajen tabbatar da magance matsalolin tsaro musamman a Arewacin Nijeriya.

Ya jaddada muhimmancin amsar gaggawa da al’amarin ke buƙata domin shawo kan al’amuran akan lokacin da ya dace.

Waɗannan dalilai sune silar da ta sanya Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya wakilci Shugaban Ƙasar a tarukan buɗe ayyukan da aka gudanar a Legas ba rikici tsakaninsa da gwamnan jihar ba kamar yadda wasu ke zargi.

By Babaji