“Ya kamata marubuta su tabbatar sun yi amfani da basirarsu wurin ciyar da Musulunci gaba”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Ci gaba daga makon jiya.
A kowacce shekara a lokaci irin wannan na Ramadan, musulmi a ko’ina a duniya na shagaltuwa da ayyukan ibada da neman kusanci da Allah, marubuta adabin Hausa su ma sukan jingine ayyukan rubuce-rubuce na nishaɗi da faɗakarwa da suke yi, zuwa ga tilawar Alƙur’ani, da faɗakarwa kan al’amuran addini, da koyar da girke-girke ga mata. A irin wannan lokaci mambobin ƙungiyar marubuta ta Jajirtattu Writers Association suna ware tsawon watan Ramadan don gudanar da shirye-shirye da suka shafi Tambayoyin Musulunci da karatun Alƙur’ani. Wannan wani ɓangare ne na ayyukan alheri da taimakon juna da ƙungiyar ta saba, domin dasa wa mambobinta tsoron Allah da son juna. A ganawar da wakilin Manhaja Blueprint Abba Abubakar Yakubu, ya yi da shugabar ƙungiyar, Malama Zainab Abdullahi da aka fi sani da Maman Ihsan, ta bayyana masa irin nasarorin da ƙungiyar ke samu, da ƙalubalenta.
MANHAJA: Waɗanne abubuwa ƙungiyarku ke gabatarwa a cikin watan Ramadan?
MAMAN IHSAN: Daga cikin shirye-shiryen da na bayyana a baya na ambaci shirin ‘Tilawar Alƙur’ani’ cikin watan Ramadan, inda muke ba da dama ga mambobin mu da ke buƙatar karanta wani ɓangare na karatun Alƙur’ani. Dama da yake bisa ƙa’idar mu a Jajirattu duk watan Ramadan mu kan tafi hutu daga fitar labarai don mayar da hankali akan ibada. Amma duk da hakan ba ma ƙasa a gwiwa wajen gabatar da waɗannan shirye-shirye a matakin bayar da gudunmawa ga addininmu. Sannan kuma akwai shirin ‘Tambayoyin Musulunci’ wanda Malam Yusuf Yahaya Gumel ke gabatarwa.
Shin kuna ganin tasirin abubuwan da ku ke yi, musamman ga masu bibiyar ku, da mambobinku?
Alhamdulillah. Gaskiya muna ganin tasirin su sosai, domin mutane kan fito su bayar da gudunmawa, har ma su koka idan ba a gabatar ba, kuma ana matuƙar ƙaruwa sosai ga dukkan shirye-shiryen da muke yi. Har ma kuma ana gabatar da satifiket ga waɗanda suka zamo na ɗaya a shirin tambayoyi.
Ku na samun haɗin kai da goyon bayan mambobin ku wajen tsara shirye-shiryen da ku ke gabatarwa?
Eh, da farko muna samun haɗin kai da goyon baya wajen tsara shirye-shiryen da muke gabatarwa, don suna ba da goyon baya sosai wajen gabatar da shiri ka’in da na’in. Kasancewar mukan raba ne kowa da abin da yake yi, ma’ana kowanne shiri aƙalla mutane uku ne ke gabatar da shirye-shiryen, wanda idan wani ba shi da lokaci wani zai gabatar. Don haka komai ke tafiya bisa tsari.
Kawo yanzu waɗanne abubuwa ne ki ka lura suna buƙatar sauye-sauye wajen tafiyar da ayyukan da ku ke yi na Ramadan da sauran harkokin ƙungiya?
To, kawo yanzu gaskiya dai babu, amma a kullum ɗan’adam kan so ya yi tunani ya kuma yi nazari kan yadda zai inganta rayuwarsa da abubuwan da yake gudanarwa. In sha Allah, muna fatan nan gaba za mu bijiiro da wasu abubuwa da za su fi wanda muke yi yanzu. Da yardar Allah za mu faɗaɗa tunani da neman shawarwari wajen tabbatar da mun gudanar da ababen da za su ciyar da al’umma gaba da kuma addininmu. Fatan mu, mu rabauta da ladan abin da muke yi, da kuma wanda Allah Ya ba mu ikon aiwatarwa.
Yaya ki ke jin daɗin tafiyar da ƙungiyar Jajirtattu, shin tafiyar da ƙungiyar marubuta na da sauƙi ko akwai wuya?
A zahirin gaskiya tafiyar da ƙungiya abu ne mai wahala, domin sai an jure, idan ba a yi haƙuri ba to, gaskiya ƙungiya za ta iya mutuwa ko ta yi sanyi. Shi ya sa na faɗa maka a baya sai da na jinginar da rubutana na tsawon lokaci, don ina son yin rubutu, amma hidimar ƙungiyar ba ya bari na. Gabaɗaya lokacina na tafiya ne a onlayin, saboda taimaka wa mambobin ƙungiyata, kafin Allah ya sa waɗanda nake yayewa yanzu suke taimaka min wajen rage min ayyukana. Don waɗanda na fara rubutu da su lokaci ɗaya sun rubuta littattafai ninkin waɗanda na rubuta, akwai da yawa da suke ba ni shawarar na daina wahalar da kaina akan mambobina, ba wani abu da za su tsinana min. Wasu ma har cewa suke yi, marubuta ƴaƴan kunama ne. Amma duk da hakan ban gajiya ba, kuma ban sare ba, na ɗauka aikin taimako nake yi, har Allah Ya kawo mu yanzu.
Wacce nasiha ki ke da ita ga marubuta a cikin wannan wata mai albarka?
Nasihata ba ta wuce marubuta su mayar da hankali ga ibada ba, su zamo masu haƙuri da zumunci, su zamo masu girmama juna da ƙaunar juna. Sannan su kaucewa shiga hatsaniya, su zamo abin kwaikwayo daga kyawawan halayen da suke rubutawa a rayuwar taurarin labaransu. Su kuma tabbatar sun yi amfani da basirar su don ciyar da al’ummar Musulmi da addinin Musulunci bakiɗaya. Su zamo masu yawan sadaka, da kyautatawa.
Me ya sa marubuta ke jingine rubutu a cikin Ramadan, akwai illa ne ga yin hakan?
Saboda mafi yawancin waɗanda ke yin wani aiki muddin ba wanda yake na wajibi ba, suna ajiye shi a gefe ne don cin moriyar azumi. Haka kuma shi rubutu na buƙatar lokaci, duba da yanayin azumi, ba kowanne marubuci ne ke iya samun cikakken lokaci ba, duba da tarin ayyuka da hidima da suke ƙaruwa. A ƙarshe, ana sallah ne don lada, mafiyawanci makaranta ba sa damuwa da karatun littafi a lokacin azumi, To, wannan shi ne ya sa rubutu ba ya tasiri da azumi, don haka muke sadaukar da rubutun da muke yi, mu rungumi ayyukan neman ibada.
Yaya ki ke fatan ganin ƙungiyar Jajirtattu ta zama nan da shekaru goma masu zuwa?
Buri da manufa suna tafiya ne kafaɗa da kafaɗa ga duk wani cikakken mutum mai lissafi. Babu shakka ina da tarin burika na ganin wannan ƙungiya ta cigaba da cimma nasorori. Ina so ta zamo wani waje da marubuta za su shigo su samu abin suke so ta fuskar ilimi, su kuma kai duk wani mataki da suke so na shahara. Ina fatan wannan ƙungiya ta zamo uwar ƙungiyoyi a ƙarƙashin ta, ta zamo abar yin magana akai, saboda cigaban da ta samar akan ayyukan adabi.
Gaya mana nasarorin da ki ka samu a matsayinki ta marubuciya.
Zuwa yanzu dai ba zan ce ga wata babbar nasara da na samu a matsayina na marubuciya ba. Sai dai na taɓa shiga gasar Hikayata ta BBC Hausa, kuma a lokacin sun tura min saƙo ta i-mel cewa suna farin cikin sanar da ni labarina ya samu nasarar shiga zagaye na gaba. Duk da cewar ban zamo cikin zakarun da suka lashe gasar ba, amma wannan ma ina yi masa kallon matakin nasara ce.
Kawo yanzu kin rubuta littattafai sun kai nawa, kuma wanne salo ki ka fi amfani da shi wajen isar da saƙon ki ga masu karatu?
Na rubuta littattafai guda bakwai ne zuwa yanzu, akwai ‘Inteesar’, ‘Adamsy’, ‘Zaman Aure’, ‘Yar Maye’, ‘Muƙaddari’, ‘Gabar Cikin Gida’, da kuma littafin ‘Makaho Ne’.
Sannan a game da salon da nake rubutu akai, zan iya cewa na fi mayar da hankali ne a game ɓangaren zamantakewar iyali da rayuwar mata, saboda a nan ne nake jin raɗaɗi, ko damuwa ko burin kawo cigaba. Duk da ina iya shiga kowanne fanni a matsayina ta marubuciya, hantsi ce mai leƙa gidan kowa, ina iya sarrafa alƙalamina ta kowanne ɓangarena rayuwa. Yawancin makaranta suna cewa ina amfani da salo mai karsashi, wato salon labarin da mai karatu zai yi ta shan ruwa, amma yana cigaba da jin ƙishirwa ba ta tare da gamsuwa ba.
Mene ne babban burinki da ki ke da shi a rayuwa?
Babban burin da nake da shi a rayuwata bai wuce rabuwa da duniya lafiya, da riskar lahira a cikin kyakkyawan yanayi na imani ba.
Wacce karin magana ce ta fi tasiri a rayuwarki?
Mahaƙurci mawadaci
Mun gode.
Ni ma ina godiya ƙwarai da gaske.
