
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Adadin ƙwallayen ɗan wasan gaba na Portugal da Al Nassr, Cristiano Ronaldo na gab da kai guda 1,000, inda ba a taɓa samun ɗan wasan da ya zura waɗanda suka kai haka ba a tarihin ƙwallon ƙafa.
A cewar tashar Sky Sports ranar Laraba bayan ya zura ƙwallo biyu a wasan neman gurbin Kofin Duniya na ƙasarsa da Hungary, jimillar ƙwallayen Ronaldo sun kai 948, wato guda 143 ga Portugal da kuma 805 ga ƙungiyoyin da ya buga wa zuwa yanzu.
Haka kuma ya zama ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a wasannin neman gurbin Kofin Duniya, lamarin da ya sa ya kere Carlos Ruiz mai guda 39 da Lionel Messi me 36 a mataki na uku.
A watan Fabarairu ne Ronaldo ya cika shekaru 40 a duniya, saidai hakan bai sa ya yi ƙasa a gwiwa ba wajen cigaba da haska wa ƙasa da ƙungiyarsa.
Sannan, ƙwallaye 32 ya ci a ƙasa da ƙungiya a shekarar 2025.
