
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hon. Adamu Atiku, wanda shi ne babban ɗan tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar kuma Kwamishinan Ci-gaban Ayyuka da Makamashi na Jihar Adamawa, ya yi murabus daga gwamnatin Fintiri.
Hakan na zuwa ne ƙasa da kwana biyu da Gwamnan Adamawan ya koma Jam’iyyar APC mai mulki.
Tuni dai kwamishinoni 22 cikin 25 da 14 cikin 21 na ciyamomin ƙananan hukumomi jihar da mahawarta na musamman suka shelanta matsayarsu ta bin gwamna zuwa APC da fara shirin ficewa daga PDP.
A wata takarda da ya aike wa Sakataren Gwamnatin jihar, Barista Awwal Tukur a yau Talata, Adamu Atiku ya sanar da gwamnan matakin nasa a hukumance.
Ya bayyana cewa, ya dauki matakin ne bisa raɗin kansa da kuma nazari akan al’amarin, yana mai bayyana shekaru bakwai da ya yin aiki a ƙarƙashin gwamnan a matsayin karamci a gare shi, inda ya yi amfani damar wajen hidimta wa jihar da al’ummarta.
Ya kuma yi wa gwamnan godiya bisa damar da ya ba shi na riƙe muƙamin kwamishinan, yana mai cewa ya ba shi ƙwarin-gwiwar aiki tuƙuru bisa jajircewa.
Sardaunan na Ganye ya bayyana cewa yana alfahari da mutanen Adamawa bisa fahimtar su da addu’o’i da tallafa masa yayin riƙe da muƙamin.
