Iran ta farmaki ofishin Netanyahu a Isra’ila

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran (IRGC) ta ce ta harba makamai masu linzami ofishin Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu da hedikwatar sojojin sama ta na ƙasar.

A wani saƙo da ta fitar ranar Litinin, rundunar ta ce za ta cigaba da fafatawa da ƙasar har sai ta samu nasara.

A ranar 2 ga Maris, 2026, ta sanar da cewa ta kai harin, inda wasu rahotanni daga Fars News Agency suka ce an yi amfani da makaman “Kheibar” wajen kai harin.

Saidai hukumomin Isra’ila sun bayyana cewa babu rahoton jikkata ko asarar rayuka a harin.

A baya-bayan nan ma an kai hare-hare a garin Beit Shemesh, inda aka samu asarar rayuka da lalacewar dukiyoyi.

Ana cigaba da jin ƙararrawar gargaɗi a sassan kudancin Isra’ila, yayin da aka tsaurara matakan tsaro a birane da dama.

Halin da ake ciki na kara tsananta duba da cewa ana sa ran matakan mayar da martani daga ɓangaren Isra’ila.

By Babaji