*Shekaru 27 jere a majalisar tarayya tun daga 1999
Daga AISHA ASAS
A cikin tarihin siyasar Nijeriya, sunan Hon. Nicholas Mutu Ebomo ya zama ɗan gida, ba baƙo ba, ba kuma mai je-ka-ka-dawo ba, ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Bomadi/Patani ta Jihar Delta ya zama ɗan majalisar wakilai mafi daɗewa a tarihin ƙasar nan, bayan ya kwashe shekaru 27 ba tare da yankewa ba a zauren Majalisar Wakilai tun daga dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999.
Tun bayan kafuwar Jamhuriya ta Hudu, babu wani ɗan majalisa da ya yi irin wannan dogon zama ba tare da tsayawa ko sauya kujera ba. Wannan nasara ta zo ne a yanayi mai cike da sauye-sauyen siyasa, rikice-rikicen jam’iyyu da tsananin fafatawa a zaɓuɓɓuka.
Mutu ya fara shiga Majalisar Wakilai ne a 1999 ƙarkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP). Tun daga wancan lokaci, ya samu nasarar sake lashe zaɓe a shekarun 2003, 2007, 2011, 2015, 2019 da kuma 2023, abin da ya nuna juriyar siyasa da kuma gagarumin goyon bayan jama’arsa.
A Najeriya, sau da dama ‘yan majalisa kan fuskanci ƙalubale daga zaɓen fidda gwani na cikin gida, rikicin shugabanci a jam’iyya ko sauyin aƙida. Sai dai Mutu ya iya tsallake waɗannan matsaloli, lamarin da ya sa ya zama abin koyi a fagen ɗorewar siyasa.
Masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa, tsayuwarsa tsawon kusan shekaru talatin shaida ce ta yadda ya iya daidaita kansa da yanayin siyasa mai cike da sauye-sauye.
Shekarar 2025 ta buɗe wani sabon babi a tafiyar siyasar Mutu. Bayan sama da shekaru ashirin a PDP, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a yanzu.
An sanar da sauya shekar tasa a hukumance a zaman majalisa, inda Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya yi maraba da shi tare da bayyana shi a matsayin ɗan majalisa mafi daɗewa a tarihin majalisar.
Da yake bayani kan dalilinsa na barin PDP, Mutu ya ce, rikice-rikicen cikin gida a matakin ƙasa da yankuna sun raunana tsarin jam’iyyar, lamarin da ya tilasta masa neman sabuwar mafita ta siyasa.
An haifi Mutu a ranar 15 ga Yuni, 1960, a Jihar Delta. Ya yi karatu a Rivers State School of Basic Studies inda ya kammala a 1986, sannan ya samu digiri daga St. Clements University, Caicos/Ireland, British West Indies a 2003.
Kafin shiga majalisar tarayya, ya taɓa zama Shugaban Karamar Hukumar Bomadi tsakanin 1996 zuwa 1997, inda ya samu gogewa a harkokin shugabanci da hulɗa da jama’a, gogewar da ta zama tubalin gina tafiyarsa a majalisa.
A tsawon zamansa na shekaru 27, Mutu ya riƙe muƙamai masu muhimmanci a kwamitoci daban-daban na majalisar. Mafi shahara daga ciki shi ne, jagorancinsa a matsayin Shugaban Kwamitin Majalisa kan Niger Delta Development Commission (NDDC) daga 2009 zuwa 2019.
A wancan matsayi, ya taka rawar gani wajen sa ido kan ayyukan ci gaban yankin Neja Delta, musamman wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana da aiwatar da ayyukan raya al’umma a yankunan da ake haƙo mai.
Haka kuma ya kasance mamba a kwamitocin Banking and Currency, Niger Delta, Governmental Affairs, Sports da Federal Capital Territory.
Baya ga aikinsa a Abuja, Mutu ya ƙaddamar da shirye-shiryen tallafa wa ɗalibai ta hanyar bada guraben karatu, shirye-shiryen ƙarfafa matasa da mata, samar da ayyukan yi, ayyukan kiwon lafiya da kuma inganta ababen more rayuwa a yankunan koguna na Bomadi da Patani.
Masu nazari na danganta nasarorinsa a zaɓe da kusancinsa da jama’a da kuma aiwatar da ayyukan da suke gani a zahiri.
Akwai alamun cewa, Mutu na iya sake tsayawa takara a 2027. Idan hakan ta tabbata, kuma ya yi nasara, zai ƙara tsawaita tarihinsa a matsayin ɗan majalisa mafi daɗewa a Majalisar Wakilai ta Najeriya.
A yau, yana ci gaba da wakiltar mazabar Bomadi/Patani ƙarkashin APC, inda tarihin zamansa na shekaru 27 ba tare da yankewa ba ya zama wata alama ta tsayin daka, dabarar siyasa da kuma ƙarfin goyon bayan jama’a.
A haƙiƙa, tafiyar Nicholas Mutu Ebomo ta zama wani babban babi a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya, babin da ke nuna cewa a siyasa, dorewa da kusanci da jama’a na iya zama ginshiƙin nasara mai ɗorewa.
