
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), ta kafa tarihi a matsayin ƙasar Larabawa ta farko da ta haramta wa yara ‘yan ƙasa da shekaru 15 amfani da kafafen Soshiyal Mediya a ƙasar.
Haka kuma, ba ta iyakance waɗanda iyayensu suka amince musu amfani da kafafen ba.
A ranar Alhamis ne majalisar zartarwar ƙasar ta ayyana haka, lamarin da ya sa ta zama ƙasar Gabas ta Tsakiya ta farko da ta yi wa yara katanga da kafafen bisa la’akari da zama barazana ga tarbiyya, shiga tattaunawar da ba su cancanta ba, yawan ɓata lokaci wajen kallon fuskar waya da fitar da bayanan kai da kai.
A sabon dokar da hukumomin ƙasar suka fitar, yaran da shekarunsu ya gaza haura adadin, ba su da ikon buɗe wani shafi a Soshiyal Mediya ko ma shiga da nufin hira, wallafa, tsokaci, raba saƙo da kuma shiga guruf-guruf ko buɗe tashoshi.
Haka kuma, wajibi ne ga kamfanonin kafafen su tabbatar da bin dokar ta hanyar hana waɗanda shekarunsu bai kai ba amfanin da fagagensu, tana mai gargaɗin soke lasisin dukkan wani kamfani da ya saɓa wa dokar.
Wannan mataki da UAE ta ɗauka ya daidai da yadda aka aiwatar a Austriliya da Birtaniya.
