
Kwamitin Masu Ruwa da Tsaki na Ƙaramar Hukumar Bichi sun ƙaddamar da wani muhimmin zama domin nemo mafita kan giɓin da aka samu game da allurar rigakafin yara daga shekarar 2019 zuwa yau, wanda aka yi wa shirin laƙabi da BCU; BIG CATCH-UP.
Kansilan Mazaɓar Fagolo kuma shugaban Majalisar Kansiloli kuma Ciyaman na Kwamitin Kula da Cigaban da aka Samu a mazaɓu dake Jihar Kano na yankin, Alhaji Habibu Musa Habibu, ya ce, shirin ingantaccen yunƙuri ne duba ga muhimmacin yara. Kuma kula da lafiyar yara babban al’amari ne da ya shafi kowa.
Shugaban majalisar kansulolin, wanda ya wakilici shugaban karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Maifata ya jaddada kafatanin kansilolin yankin tuni suka yi ɗamarar bai wa wannan shiri gudunmawa yadda yakamata, ta hanyar ba da lokacinsu tare da aiki da mambarin malamai wajen wayar da kan jama’ar yankunansu na mazaɓu 11, domin ma’aikatan da za su gudanar da wannan aiki, su aiwatar da shi a cikin nasara da kwanciyar hankali.
“Duk abin da wannan furogiram ɗin nan yake buƙata a Bichi; Ciyaman zai yi ɗari bisa ɗari ba tare da wani naƙasu ba, in sha Allahu. Kuma za mu yi aiki tuƙuru don ganin al’umma sun ba da haɗin kai, an tabbatar da duk wanda yakamata a yi masa rigakafin an yi masa.” Alhaji Habibu Musa Habibu.
A nasa ɓangaren Jami’in Kula da Harkar Sadarwa da Walwala na Sashen Lafiya dake Bichi, Malam Nura Ibrahim Abubakar, ya bayyana wannan muhimmin shiri, yana zuwa ne daga matakin ƙasa da jiha zuwa ƙananan hukumomi ta hanyar samar da shawarwari, domin ganin an cim ma nasarar cike gurbin da aka samu na yara da ba’ayi wa allurar rigakafin (Routine Immunization).
Ya kuma ce, yana daga manufar shirin, gano adadin ɗaukacin yaran da suka rasa allurar rigakafin tun daga matakin farko, musamman a lokacin annobar cutar Korona da ta janyo rufe asibitoci wanda hakan ya haddasa da yawa iyayen yara ba su samu damar kai ‘ya’yansu asibitoci yi musu allurar rigakafin da har wa yau ba a yi musu ba, kuma rashin allurar rigakafin kan iya haifar da naƙasu ga lafiyar yara.
“Da akwai cututtuka da yawa waɗanda aka daƙile su ta hanyar rigakafi, a yau babu su a doron ƙasa. Idan yau aka yi sikifin gida ɗaya ba a yi musu rigkafi ba, matuƙar akwai masu cuta mai yaɗuwa a cikinsa za ta ci gaba da yaɗuwa ne kamar wutar daji; wannan ya ba wancan, wancan ya ba wannan, mafi yawan cututtuka da haka suke yaɗuwa. Idan muka kawar da foliyo daga doron Nijeriya, mun bar ta ke nan!” Malam Nura Ibrahim Abubakar.
Don haka hukumomin lafiya tare da wasu ƙungiyoyi na jama’a da kuma gwamnati suka bijiro da wannan gangamin shiri domin tabbatar da an yi wa irin waɗannan yara allurar rigakafin da suka rasa a baya, domin bunƙasa lafiyarsu; suma su rayu a cikin ƙoshin lafiya da kuzari da kuma walwala da jin daɗi.
Kazalika wannan zama da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Bichin, ya samu kyakkyawan fasali na kyautata zaton kwalliya na gab da biyan kuɗin sabulu, bisa la’akari da nagartattun shawarwari da aka samu daga kowane ɓangare na masu ruwa da tsakin yankin, domin cim ma muradin nasarar wannan aikin.
Taron ya haɗar da; wakilin Shugaban Sashen Lafiya a matakin Farko, Sakataren Hakimin Bichi Galadiman Kano, wakilin Dagacin Bichi, wakilin Limamin Bichi, Kwamandan Hisba, Kwamandan Bijilanti, NOA , Women Development Centre, FOMWAN Amira, LGA Consultant, ACSM FP SARMAAN II Sunday Joshua, CAN Postor Rev. Ugwuabuchi Charles.


