Ƙungiyar Poetic Wednesdays ta gudanar taron Eid Pop-Up a ranar Asabar, 6 ga Yuni, 2026, domin bikin cika shekaru goma da kafuwarta tare da bayyana sabon jigon bikin Kano International Poetry Festival (KAPFEST) karo na uku, mai taken “Reclaiming Languages”, wato ɗabbaka yaruka.
An gudanar da taron ne a Alliance Française da ke Kano, inda ya haɗa mawaƙan baka, marubuta, masu sha’awar adabi da sauran jama’a domin tattaunawa, nazari da kuma nishaɗantarwa ta hanyar fasaha. Taron ya kasance wata dama ta waiwayen nasarorin da ƙungiyar ta samu cikin shekaru goma da kuma bayyana shirye-shiryenta na gaba.
A yayin taron, an gabatar da waƙoƙin baka da tare da wani zaman tattaunawa da ya mayar da hankali kan muhimmancin harsuna a matsayin taskar tarihi, al’adu, asali da tunanin al’umma. Tattaunawar ta samu halartar Daraktar Gudanarwa ta Poetic Wednesdays Initiative, Naseeba Babale, da Nana Sule, yayin da ɗan jarida Misbahu El-Hamza ya jagoranci zaman.
Masu tattaunawar sun jaddada muhimmancin kare harsunan gida da kuma farfaɗo da su a daidai lokacin da ake fuskantar barazanar gushewar wasu harsuna sakamakon ƙaruwar tasirin manyan harsunan duniya. Sun kuma yi bayani kan rawar da marubuta, masu fasaha, malamai da al’umma ke takawa wajen tabbatar da cewa harsuna sun ci gaba da rayuwa.
Haka kuma, mawaƙan baka da suka haɗa da Hidaya Mahmud, Hafsat Ismail da Mujahid Abdulaziz da sauran su sun gabatar da waƙoƙi da suka yi daidai da jigon taron, inda suka nuna yadda harshe ke da alaƙa da tarihi, tunani da kuma rayuwar al’umma.
Da yake jawabi a wajen taron, wanda ya kafa ƙungiyarPoetic Wednesdays Initiative, Malam Salim Yunusa, ya bayyana cewa ƙungiyar ta fara ne daga wata alama ta hashtag a Facebook.
Ya ce, “Tsawon shekaru goma, Poetic Wednesdays ta samar da sarari da gurbi ga mutane domin su ba da labarunsu, su bayyana abubuwan da suka fuskanta tare da musayar sabbin tunani ta hanyar fasaha. Jigon ‘Reclaiming Languages’ yana tunatar da mu cewa harshe ba hanyar sadarwa kawai ba ce, illa wata taskar rayuwa da ke bayyana ko su waye mu da yadda muke fahimtar duniya.”
Ƙungiyar ta kuma yaba wa mawaƙan baka, masu sa kai, abokan hulɗa da masu goyon baya da suka taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban ta cikin shekaru goma da suka gabata.
Bikin KAPFEST 3.0 da za a gudanar a watan Oktoban 2026 zai tattaro marubuta, mawakan baƙa, masu fasaha, masana da masu sha’awar adabi daga sassa daban-daban na Najeriya da sauran ƙasashe domin tattaunawa kan batutuwan harshe, asali, fassara, adabin baka, tarihi da makomar harsunan Afirka a duniyar da ke ci gaba da sauyawa.
Poetic Wednesdays Initiative kungiya ce da ke inganta adabi, waƙa, ba da labari da tattaunawa kan muhimman batutuwan zamantakewa ta hanyar karatu, horaswa, bukukuwa, shirye-shiryen jagoranci da ayyukan hulɗa da al’umma, musamman matasa.
