Adamawa: Buhari ya jajanta wa al’ummar Kwapre bisa harin ta’addanci

Daga WAKILINMU

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna alhininsa tare miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar Kwapre da ke yankin ƙaramar hukumar Hong, jihar Adamawa, dangane da harin da mayaƙan Boko Haram suka kai musu kwanan nan.

Buhari a bisa wakilicin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya miƙa ta’aziyyarsa ne yayin ziyarar da sakataren ya kai a yankin da lamarin ya shafa.

A cewar Boss Mustapha, “Na zo Kwapre ne a bisa umarnin Shugaba Muhammadu Buhari domin ganin abin da ya auku. Shugaban ya jajanta muku kan abin da ya faru.”

Ya ce, “Na gani da idona irin ɓarnar da aka tafka muku, na yi matuƙar baƙin ciki kan ɓarnar da na gani, amma ina mai ba ku tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya za ta yi abin da ya kamace ta wajen kare rayuwar mutane da dukiyoyinsu.”

Mustapha ya bayyana cewa daga bayanan da ya samu, an lalata gidaje sama da 78 da shaguna 12 da makarantu haɗa da wuraren Ibada.

Yana mai cewa sha’anin kare rayuwar al’umma abu ne da ya shafi kowa bai wai gwamnati kaɗai ba. Tare da cewa jama’a na da rawar da za su taka dangane da bada tsaro a mazauninsu.

Daga bisani, Sakataren ya ce Gwamnatin Tarayya za ta yi dukkan mai yiwuwa domin hana aukuwar haka a gaba. Kana za ta tallafa wajen gyara wuraren da aka lalata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *