ADC ta roƙi Kotun Ɗaukaka Ƙara ta hana INEC sauya shugabanci da ‘yan takararta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar adawa ta ADC, ta buƙaci Kotun Ɗaukaka Ƙara ta hana Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) sauya mata rahotannin shugabanci da takardun bayanan ‘yan takarar shugaban ƙasa da na gwamnoni har zuwa lokacin da za ta yi hukunci akan ƙorafin ADC game da hukuncin Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya.

Jam’iyyar ta shigar da ƙorafe-ƙorafe guda 17 da ke ƙalubalantar hukuncin na ranar 5 ga Nuwamba, 2026, wadda ta bayyana a matsayin kuskure a dokance, tana mai cewa kotun ba ta da ikon yin hukunci kan rikicin jagorancinta. Daraktan dabarun sadarwa na kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC, Phrank Shaibu ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a ranar Talata.

ADC tana kuma ƙalubalanci hukuncin da aka yi a baya da ya ba wa Bala Gombe damar gyaran ƙorafe-ƙorafensa duk da cewa akwai rashin amincewa da ikon kotun kan yin hukuncin al’amarin.

Jam’iyyar ta koka kan cewa barin INEC ta aiwatar da hukuncin kotun na ranar 5 ga Nuwamban gabanin Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta yi hukunci kan matakin nasu ka iya jefa korafinsu da ‘yan takararsu cikin halin rashin tabbas. Akan haka ne ta roƙi kotun da ta tsare bayanan jagoranci da na ‘yan takarar har zuwa lokacin da za a warware rikicin shari’ar shugabancin jam’iyyar.

Hukuncin Mai Shari’a Lifu na Babbar Kotun na ranar 5 ga Nuwamba ga ƙarar da Nafi’u Bala Gombe ya shigar, ya sake jefa tsarin jagorancin jam’iyyar da shirye-shiryenta ga zaɓen 2027 a cikin halin rashin tabbas musamman ganin zaɓen na 2027 ke cigaba da ƙaratowa.

By Babaji

Leave a Reply