Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, a matsayin take haƙƙin ɗan adam mai tsanani.
Jam’iyyar ta ce ana tsare da El-Rufai a hannun Hukumar ICPC tsawon kwanaki sama da 30, lamarin da ta bayyana a matsayin wanda ya saba doka da kundin tsarin mulki.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja ranar Laraba, ADC ta zargi hukumomin tsaro da ƙoƙarin tilasta wa El-Rufai sauya matsayinsa na siyasa ta hanyar matsin lamba.
Jam’iyyar ta bukaci ICPC da ta mutunta dokar ƙasa ta hanyar sakin El-Rufai nan take domin ya samu damar shirya kansa don kare kansa a gaban kotu.
Ta kuma jaddada cewa tsare mutum ba tare da gabatar da shi gaban kotu ba na tsawon lokaci alama ce ta mulkin kama-karya, wanda bai dace da tsarin dimokuraɗiyya ba.
Saboda haka, ADC ta yi barazanar kai ƙara ga ƙungiyar Amnesty International da sauran ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam idan har ba a saki El-Rufai ba cikin gaggawa.
Sanarwar ta ƙara da cewa, kimanin kwanaki 32 da suka gabata ne El-Rufai ya amsa gayyatar EFCC cikin lumana, amma bayan kwanaki biyu da sakinsa, sai ICPC ta sake kama shi, kuma har yanzu bai fuskanci shari’a ko tuhuma a hukumance ba.
Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa ana hana shi ganawa da iyalansa da likitansa, tare da matsa masa lamba ya yi watsi da ’yancin sa na siyasa domin samun ’yanci.
ADC ta bayyana cewa wannan ba aikin doka ba ne, illa amfani da hukumomin gwamnati wajen dakile harkokin siyasa, wanda ta ce ya saba wa ka’idojin dimokuraɗiyya da kundin tsarin mulki na Nijeriya.
