ADC tsagin David Mark ta nemi kotu ta soke matakin INEC akan jam’iyyar

Spread the love

Jam’iyar adawa ta ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark, ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda ta roƙi kotu da ta soke matakin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ɗauka na cire amincewarta a hukumance.

A cikin ƙarar da ke gaban Mai Shari’a Emeka Nwite, Mark ya kuma roƙi kotu da ta bayar da umarnin gaggawa na soke matakin da INEC ta ɗauka na ƙin halartar ko sa ido kan tarukan jam’iyyar har sai an kammala sauraron shari’ar.

Haka kuma ya nemi umarni da zai tilasta INEC ta mayar da sunayen dukkan mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na ADC a cikin rajista da shafin ta na yanar gizo, kamar yadda suke kafin a shigar da ƙarar, har sai an yanke hukunci a shari’ar gaba ɗaya.

Wannan ƙara ta biyo bayan matakin da INEC ta ɗauka a ranar 1 ga Afrilu na cire sunayen David Mark da Ogbeni Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakatare na ADC daga shafinta na yanar gizo.

Wannan mataki ya biyo bayan hukuncin Kotun Ƙoli na ranar 12 ga Maris akan wata ƙara da Hon. Nafiu Bala Gombe ya shigar a gaban Mai Shari’a Nwite na kotun.

Ƙarar, wadda ta ƙunshi buƙatu uku, an shigar da ita bisa tanade-tanaden Dokar Tsarin Ayyukan Kotun Tarayya tare da ikon kotu na asali da kuma ikon ta na adalci wajen bayar da umarnin gaggawa.

Daga cikin buƙatun akwai “umarnin gaggawa na soke matakin ko umarnin da wanda ake ƙara (INEC) ya ɗauka na cire sunayen Kwamitin Gudanarwa na jam’iyyar daga shafinta na hukuma, da kuma ƙin halartar ko sa ido kan tarukan jam’iyyar, har sai an yanke hukunci a shari’ar.”

Lauyan ya ƙara da cewa INEC, bisa kuskuren fahimtar umarnin Kotun Ƙoli, ta cire sunayen wannan shugabanci daga shafinta.

A cewarsa, akan haka ne hukumar zaɓen ta ɗauki matsayar ƙin amincewa da shugabancin, lamarin da ya haifar da giɓi a tsarin shugabancin jam’iyyar ADC.

By Babaji