A cikin shekarun baya-bayan nan, karɓar bashi ta hanyar manhajojin yanar gizo ya zama ruwan dare a Nijeriya, musamman a tsakanin matasa da masu sana’o’i. Duk da ƙorafe-ƙorafe da ake yawan ji kan tsananin ruwa da kuma matsin lamba daga masu ba da lamunin, har yanzu mutane da dama na ci gaba da rungumar wannan hanya domin warware matsalolin rayuwa na gaggawa. Wannan lamari na nuna cewa akwai babbar matsala da ke buƙatar a duba ta da idon basira.
Babu shakka, bunƙasar harkar fasahar kuɗi, wato fintech, ta kawo sauƙi wajen samun bashi cikin sauri. Amma a gefe guda, wannan sauƙi ya buɗe ƙofa ga wasu kamfanoni marasa tausayi da ke anfani da halin ƙuncin jama’a wajen jefa su cikin mawuyacin hali. Ruwan da ake ɗora wa irin waɗannan bashin na da tsanani matuƙa, wanda kan sa mutum ya biya ninki fiye da abin da ya karɓa cikin ɗan lokaci kaɗan.
Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda wasu masu karɓar bashi ke faɗawa cikin tarkon “bashi kan bashi”. Wato mutum ya karɓi rance daga wata manhaja domin biyan wata, lamarin da ke ƙara masa nauyi da damuwa har ya kasa fita daga wannan hali. Wannan yanayi na jefa mutane cikin talauci da kuma matsananciyar damuwar tunani.
Haka kuma, akwai matsalar cin zarafi da tauye haƙƙin masu karɓar bashi. Rahotanni sun nuna cewa wasu kamfanonin na amfani da bayanan sirri wajen matsa wa kwastomomi lamba, har ma su wulaƙanta su a kafafen sada zumunta. A wasu lokuta ma, ana zargin su da ƙirƙirar saƙonnin ƙarya domin kunyata wanda ya kasa biyan bashi. Wannan ba wai kawai rashin ɗabi’a ba ne, har ma take haƙƙin ɗan adam.
Dalilin da ya sa mutane ke faɗewa wannan hali ba ya rasa nasaba da matsin tattalin arziki. Yawancin masu karɓar irin wannan bashi suna yin haka ne saboda matsalolin gaggawa—kamar rashin lafiya, buƙatun iyali ko kuma ƙoƙarin farfaɗo da kasuwanci. Amma rashin cikakken bayani game da sharuɗɗan lamuni da kuma tsadar ruwa na sa su shiga cikin halin da ya fi wanda suke ƙoƙarin gujewa muni.
A wannan gaɓar, rawar da gwamnati za ta taka na da matuƙar muhimmanci. Duk da matakan da wasu hukumomi ke ɗauka wajen daidaita harkar, har yanzu akwai giɓi wajen sa ido da kuma hukunta kamfanonin da ke karya doka. Wajibi ne a ƙara tsaurara dokoki da tabbatar da cewa duk masu ba da lamuni suna aiki ne bisa ƙa’ida, tare da kare haƙƙin masu amfani.
Sai dai kuma, alhakin ba ya tsaya ga gwamnati kaɗai ba ne. Ya rataya a wuyan jama’a su kasance masu hankali kafin su ɗauki irin wannan mataki. Karɓar bashi ba wajibi ba ne, musamman idan babu tabbacin yadda za a biya. Yana da kyau mutane su nemi hanyoyin samun taimako daga iyalai, abokai ko cibiyoyin kuɗi masu aminci kafin su rungumi irin waɗannan manhajoji.
A ƙarshe, ya zama wajibi a fahimci cewa sauƙin samun bashi ba lallai ne ya zama alheri ba. Idan ba a yi taka-tsantsan ba, zai iya zama tarkon da zai jefa mutum cikin matsananciyar wahala. Don haka, gujewa karɓar rance daga manhajojin da ba a tantance su ba, tare da yin nazari mai zurfi kafin ɗaukar bashi, shi ne mataki mafi dacewa domin kare kai da makomar rayuwa.
