Tinubu ya yi jimamin mutuwar janar na soja a harin Benisheikh, ya ce sadaukarwarsu ba za ta tafi a banza ba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu, ya bayyan alhininsa akan rasuwar sojojin rundunar 29 Task Force Brigade na Operation HADIN KAI da suka mutu a harin ta’addanci a Benisheikh da ke Arewa ta Gabas.

Ya miƙa ta’aziyya ga rundunar soji da iyalan mamatan, tare da yabawa jarumtakar su wajen kare al’umma daga hare-haren ‘yan ta’adda. Shugaban ya ce harin alama ce ta raunin ‘yan ta’addan, yana mai jaddada cewa sojoji na cigaba da samun nasara a farmakin da suke kaiwa.

Tinubu ya ƙarfafa gwiwar dakarun gaba da su ci gaba da aiki da jajircewa, yana tabbatar da cikakken goyon bayan gwamnati ga rundunar soji.

Haka kuma, ya buƙaci ‘yan Najeriya da kafafen yaɗa labarai su mara wa sojoji baya, yana mai cewa waɗannan sojoji jarumai ne da ba za a taɓa mantawa da su ba.

A ranar Laraba Brigadier-General O. Braimah, ya rasa ransa sakamakon harin Boko Haram a sansanin soja na Benisheikh, cikin Karamar Hukumar Kaga da ke Jihar Borno.

Braimah ya rasa rasu ne yana aikin soja, tare da wasu sojoji da dama, ciki har da Imam ɗin rundunar. Rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe wasu daga cikin ‘yan ta’addan Boko Haram yayin fafatawar.

By Babaji