AFCON 2025: Nijeriya ta doke Masar a wasan neman matsayi na uku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Asabar ne Super Eagles ta Nijeriya ta yi nasarar doke takwararta ta Masar da ci 4 da 2 a zangon buga fenariti, lamar da ya ba ta damar samun kyautar karramawa ta wanda ya samu matsayi na uku a Gasar kofin ƙasashen Nahiyar Afirka (AFCON) na 2025 da ke gudana a Moroko.

An tashi wasan ne bayan minti 90 ba tare da ɗaya daga cikin ɓangarorin ya samu damar zura ƙwallo a raga ba, inda hakan ya tilasta musu shiga zangon fenariti.

Mai tsaron gida na Nijeriya Stanley Nwabali ya sake nuna bajinta sakamakon kare bugun Mohamed Salah da Oumar Marmoush na Manchester City.

Wannan shi ne karo na tara da Super Eagles ke yin nasara a wasan neman matsayi na uku a AFCON.

An yi wannan wasa ne bayan da Moroko mai masauƙin baƙi ta doke Nijeriya a wasa dab da na ƙarshe, yayin da ita Masar ta sha kaye a hann Senegal da ci 1 da nema.

A gobe Lahadi ne za a fafata tsakanin Moroko da Senegal a wasan ƙarshe na AFCON.

By Babaji