Kano: An yi wa uwa da ‘ya’yanta shida kisan gilla a gidansu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Al’umma a Jihar Kano sun shiga jimami yayin da wani mummunan hari ya yi sanadiyyar mutuwar mahaifiya da ‘ya’yaynta guda shida, lamarin da mazauna yankin suka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin ababe mafi tsoratarwa da suka faru a baya bayan nan.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da rasuwar mutane bakwai ciki har da matar mai suna Fatima Abubakar kuma mai shekaru 35 da ‘ya’yan nata shida a yau Asabar a yayin wani mummunan farmaki a gidansu da ke Ɗorayi Charanchi Quarters a garin Kano.

A cewar ‘yan sandan, makasan, waɗanda ba a kai ga gano su ba, sun kutsa cikin gidan ne ɗauke da wasu muggan makamai, waɗanda suka yi amfani da su wajen yi wa ‘yan gidan munanan raunuka.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin a wata sanarwa, Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Kiyawa ya ce ofishinsu ya samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 12:10 na rana, inda aka ruwaito al’amarin, wanda ya auku a gidan wani mai suna Haruna Bashir.

Jin haka ya sanya Kwamishinan ‘yan sandan, Ibrahim Bakori ya aike da tawagar jami’ai ƙarƙashin jagorancin mataimakinsa na ɓangare ayyuka, DCP Lawal Mani.

Kiyawa ya ƙara da cewa, tuni aka garzaya da gawarwakin mamatan zuwa asibitin Murtala Mohammed, inda aka tabbatar da mutuwar dukkan su.

Rundunar ta kuma umarci sashen binciken manyan laifukanta da ya gaggauta fara bincike domin gano da kama waɗanda ke da hannu a farmakin.

A ƙarshe, rundunar ta miƙa saƙonta na ta’aziyya ga iyalan mamatan, mazauna Ɗorayi Chiranchi Quarters da ɗaukacin al’ummar Kano, tana mai cin alwashin farauto masu laifin da gurfanar da su a gaban shari’a.

By Babaji