Afirka ta Kudu: An sake buɗe binciken kisan ’yan gwagwarmayar mulkin wariya

Spread the love

A ranar Litinin, wata kotu a Afirka ta Kudu ta buɗe sabon bincike kan kisan gilla da jami’an ’yan sanda suka aikata shekaru 40 da suka wuce a kan wasu fitattun ’yan gwagwarmaya huɗu da ake kira Cradock Four, a ɗaya daga cikin munanan laifukan mulkin wariyar launin fata (apartheid) da aka fi tsana a tarihin ƙasar.

Mutanen da abin ya shafa sun haɗa da malaman makaranta Fort Calata, Matthew Goniwe da Sicelo Mhlauli, da kuma wani ma’aikacin layin dogo mai suna Sparrow Mkonto. An yi garkuwa da su tare da kashe su yayin da suke komawa gida daga taron siyasa a garin Cradock da ke kudu maso yammacin ƙasar.

Bayan shekaru da dama da kisan ya faru ba tare da hukunta wani ba, iyalan waɗanda aka kashe sun zargi gwamnatin da ta zo bayan kifar da tsarin wariyar launin fata da hana shari’ar kaiwa ga kotu. Lauya Howard Varney, wanda ke wakiltar iyalan mutanen, ya shaida wa kotun da ke Gƙeberha cewa, wannan na iya zama dama ta ƙarshe da iyalan za su samu don ganin an tabbatar da gaskiya da adalci.

“Bayan shekaru 40, iyalai har yanzu suna jiran adalci da kwato haƙƙi daga abinda aka yi masu. Za mu nuna wa kotu cewa wannan kisan gilla na Cradock Four ya kasance shiri ne na gwamnati a matakin koli na hukumar tsaro a lokacin tsarin wariyar launin fata,” inji Varney.

Kotun Gƙeberha ita ce ke sauraron wannan shari’a karo na uku tun bayan faruwar lamarin a shekarar 1985, a lokacin da gwamnatin farar fata ke murƙushe masu adawa da tsarin mulkinsu.

An kafa Hukumar Gaskiya da Sasanci (Truth and Reconciliation Commission) a shekarun 1990s domin tantance laifukan siyasa da suka faru a lokacin mulkin wariyar launin fata. Amma hukumar ta ƙi ba da afuwa ga wasu mutum shida da ake zargi da kisan Cradock Four. Hakan ya bar musu damar gurfana a gaban kotu, amma gwamnati ta kasa ɗaukar mataki, a cewar Varney.

 “Akwai alamun gazawa ta fuskar sakaci, rashin kulawa, ko kuma rashin iya gudanar da bincike. Amma kuma iyalan suna zargin cewa, wasu ’yan siyasa sun tsoma baki domin hana shari’ar ci gaba,” inji shi.

Bayan koke-koke da aka daɗe ana yi, Shugaba Cyril Ramaphosa ya kafa kwamitin bincike a watan Afrilu domin duba jinkirin da ake yi wajen gurfanar da waɗanda suka aikata laifuka a lokacin mulkin wariyar launin fata.

A watan Janairu kuwa, iyalan waɗanda aka kashe 25 ciki har da iyalan Cradock Four suka shigar da ƙara a gaban kotu, suna tuhumar gwamnati da gaza yin bincike da gurfanar da masu laifi, lamarin da suka ce ya kasance “gagarumar gazawa” da ta ci zarafin mutuncin iyalansu da waɗanda aka zalunta.

Varney ya jaddada cewa, “Wannan bincike na yanzu wataƙila shi ne damar ƙarshe da iyalan za su samu don samun abinda zai kwanciyar masu da hankali. Sun cancanci cikakken bayani da bayyana gaskiya game da abin da ya faru.”

By ukarofi