Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Kungyar ɗalibai mata ta Arewa da ake kira Arewa Female Student Association AFSA, ƙarƙarshin shugabancin Fatima Abdullahi ta karrama DPM Mahamoud Lamiɗo Babban Daraktan kuɗi da mulki na ƙaramar hukumar birni KMC, Kano, kuma shugaban ƙungyir darkotocin kuɗi mulki na Kano, a taron da ya gabatar a ɗakin taro na KMC.
A jawabinta shugabar AFSA Fatima A A.ta ce sun karrama DPM Mahamoud Lamiɗo saboda ƙwarewar aiki da nasarorin da ya samu a ɗan ƙanƙanin lokaci.
Shi ma a nasa jawabin DPM Mahamoud ya ce wanan karramawa abin godiya ne ga Ubangiji da yabawa iyayensa kan tarbbiyar da ya samu daga gare su, domin a cewarsa su ne sanadin samun wannan ɗaukaka da nasarori a rayuwarsa. Ya ƙara da cewa wananan kujera ta DPM ta yi wa kowa adalci ne a kowace jam’iyya yake duk kasacewar shi ɗan Kwamkwasiyya ne amma burinsa a haɗa kai da kowanne ɗan jam’iyya domin zaman lafiya da kwanciyar hankali “kasancewar mu dukkkanin mu Musulmi ne bai kamata wani logon banza ya haɗamu gaba ba kuma nake ta ƙoƙari na ga an zama abu ɗaya duk da bambancin siyasa a tsakaninmu.”
A ƙarshe ya yaba wa jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamanan Kano Alhaji Abba Kabir Yusif kan ba shi wannan muƙami da ya yi wanda ya bashi damar yi wa jama’a masu yawa samun tallafin kuɗi na miliyan guda-guda kimanin mutane ɗari da kuma wasu ɗaruruwan dake neman tallafi yanzu haka ga kuma tallafi iri-iri daga gwamnatin Kano take yi kuma ta basu dama a ɓangarori da dama musamman ɓangaren waɗanda suka samu matsalar rusau sakamakon ruwan damuna da dai sauransu, inda ya ce dole su kyautatawa jama’a su tausaya musu musamman ganin yadda suka taso a gaban Galadiman Kano wanda kullum aikinsa gina al’umma kamar yadda gwamnatin Kano ta sa gaba a wannan lamari na gina jama’a.
