Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Shirin ƙarfafa ilimin ’yan mata da ƙarfafa su (AGILE) ya miƙa sabon aikin gine-gine ga makarantar sakandaren ƙaramar hukuma ta gwamnati (GJSS) da ke Akko Gari, a Jihar Gombe, domin inganta yanayin karatu da ƙara wa ’yan mata damar samun ilimi mai inganci.
An miƙa aikin ne bayan hukumomin da abin ya shafa sun tabbatar da kammalawa da ingancin aikin, inda aka bayyana cewa an tsara shi ne domin samar da muhalli mai aminci da dacewa da koyarwa da koyo.
Kodinetan AGILE na Jihar Gombe, Dr Amina Haruna Abdul, ce ta jagoranci tawagar da ta miƙa aikin, tare da kwamishinan ilimi da babban sakatare na ma’aikatar.
Da take jawabi a wajen bikin, tawagar AGILE ta ce aikin na daga cikin matakan da shirin ke ɗauka domin inganta gine-ginen makarantu da samar da yanayin da zai ƙarfafa ’yan mata su ci gaba da karatu tare da samun kyakkyawan sakamako.
Tawagar ta kuma raba kayan koyarwa da na koyo ga ɗaliban makarantar domin tallafa wa aikin malamai da sauƙaƙa karatu ga ɗalibai.
Haka kuma, an buƙaci kwamitin kula da makaranta (SBMC) da al’ummar makarantar su ɗauki nauyin kula da ginin tare da tabbatar da tsafta, amfani da shi yadda ya kamata da kuma ɗorewarsa.
AGILE ya ce aikin na daga cikin shirye-shiryensa na ci gaba da inganta ababen more rayuwa a makarantu, ƙara ingancin koyo da kuma faɗaɗa damar ’yan mata samun ilimi a faɗin Jihar Gombe.
Shirin ya kuma yi daidai da ajandar gwamnatin Jihar Gombe ta kawo sauyi a fannin ilimi, musamman ta hanyar inganta muhalli da yanayin karatu da kuma ƙara yawan ’yan mata da ke samun damar zuwa makaranta.
