Aiwatar da sabuwar dokar haraji a 1 ga Junairu na bisa tsari, inji Fadar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa kuma Shugaban kwamitin Shugaban Ƙasa akan lamuran kasafi da gyare-gyaren haraji, Taiwo Oyedele ya ce ranar ɗaya da ga watan Junairun 2026 da aka ayyana aiwatar da sabuwar dokar haraji tana nan daram.

Oyedele ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a Legas yayin ganawa da manema labarai bayan wata ganawa ta musamman da Shugaba Bola Tinubu.

Ya bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya ba za ta ja da baya ko sassauta matsayinta ba wajen aiwatar da sabuwar dokar haraji da aka tsara fara aiki da ita a farkon watan Janairun 2026 ba.

Gwamnatin ta kuma ce dokar na daga cikin manyan tsare-tsaren da aka shimfiɗa domin gyara tsarin haraji na ƙasa, faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga, da kuma rage dogaro da bashin waje.

A cewarsa, duk da korafe-korafen da wasu sassa ke yi, za a aiwatar da dokar ne bisa tsari da adalci, tare da la’akari da halin da ƴan ƙasa ke ciki, domin tabbatar da ɗorewar tattalin arziƙin ƙasa da ci-gabanta.

By Babaji