Abinda iyayen yanzu suka ɗauka jin daɗin aure shi ne namiji ya ke kashewa ɗiyarsu kuɗi kafin ya aureta da bayan ya aureta. Wannan a wajensu shi ne so. kuma shi ne jin daɗin aure.
Hakan ya sa su ma matan da yawa suka tafi akan wannan tsarin.
Su kuma maza sai su ke amfani da wannan damar wajen cuta da gallazawa matan saboda ganin abin hannunsu su ke so ba ainahin su kansu ba a zallar asalin ɗan adamtaka. Shi ya sa a yanzu babu girmamawa ga wasu mazan ga surukansu.
A da surukai kamar iyaye ne ana girmamasu kamar yadda ake girmama iyaye. Amma yanzu da kwaɗayi ya bayyana da kuma kowa na son nasa, Sai abubuwa suka canja.
Allah Ya datar damu, ya sa a kiƙa soyayya don Allah, a kuma girmama juna don Allah.
Duk wanda zai gina rayuwar aurensa ya nemi daidai shi kar ya biyewa son zuciyarsa daga ƙarshe shi ne ake yin nadama.
Gidan aure ya zama babu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kullum ana cikin ƙorafi da kai kuka ga iyaye da kuma kafofin sada zumunta ana ‘Hide My ID’.
A da matsalolin mutane ana gabatar da su ne ga malaman addini su ma ka addu’a ko su ba ka addu’ar ka yi da kanka. Amma yanzu an dawo da ita soshiya midiya.
A da mata basa sakaci da addu’a akan matsalolinsu na zamantakewar aure. Amma yanzu sun yi sakaci sun bar addu’ar sun dawo da komai nasu soshiyal midiya.
Zan cigaba da zaƙulo muku wasu matsalolin musamman waɗanda suka shafi zamantakewar aure da yadda za a gyara. Idan da hali ma a kiƙa faɗin addu’o’in da mutum zai yi da kansa ba sai ya je wajen boka ko malam ba, ko ya kawo mana ƙorafinsa nan soshiya mediya ba.
ABDULLAHI JIBRIL DANKANTOMA (Uncle LARABI), 08065418892. ( Don Allah, WhatsApp kawai banda kira).
