Al’adarmu ta Arewa ba ta gamsu da ganin mace tana ƙwallon ƙafa ba – Aisha Kissar

Spread the love

 

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Aisha Kissar wata matashiya ce a Jihar Kano, wacce ta kasance ɗaya daga cikin tsirarun mata masu sha’awar ƙwallon ƙafa tun tana yarinya. Wani abu da ya ƙara sa Aisha ta zama daban da sauran ‘yammata shi ne duk da yadda take son ƙwallon ƙafa ba ta wasa da sha’anin karatu, na boko da na addini, don yanzu haka tana da haddar rabin Alƙur’ani a kanta. Kuma duk da cewa tana son harkar wasannin motsa jiki, amma ba ta bari son zuciyarta ya shiga tsakaninta da iyayenta ba, waɗanda suke nuna wasan ƙwallon ƙafa bai dace da ‘ya mace kamar ta ba. Aisha da ke sha’awar kallon wasan Kano Pillars da Real Madrid tana fatan ganin wata rana an samu ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata a Arewa. 

MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki.

AISHA KISSAR: Da farko dai cikakken sunana Aisha Isah Musa, amma an fi sanina da Aisha Kissar a zaurukan sada zumunta. Ni ɗaliba ce, mai sha’awar wasan ƙwallon ƙafa.

Ko za ki gaya mana tarihin rayuwarki?

An haife ni a Jihar Yobe a ƙaramar Hukumar Potiskum a shekarar 2008, a Unguwar Fursuna. Bayan mun dawo Kano da zama sai aka sa ni a makarantar firamare ta Arƙam Bin Arƙam. Bayan na kammala sai na shiga makarantar sakandire ta GASS Nasiru Ahali, inda Allah ya bamu ikon kammalawa a wannan shekara ta 2024. Sannan har yanzu ina cigaba da karatun Islamiyya a Madarasatul ɗauhatus Subyan, inda nake neman haddar Alƙur’ani mai girma, yanzu haka ina da haddar izifi 30. Alhamdulillah. 

Tun yaushe ki ka fara sha’awar harkar ƙwallon ƙafa?

Gaskiya tun ina ƙarama a makarantar firamare nake sha’awar ƙwallon ƙafa sosai, saboda yadda nake ganin mazan makarantar na buga ta, har ma ta kai na kan shiga cikinsu ni ma a buga ta da ni. 

Wato dai ashe kema kina taɓa buga ƙwallon kafar?

E, gaskiya kamar yadda na faɗa maka a baya lokacin ina firamare na ɗan taɓa bugawa, daga baya kuma nakan buga a cikin gida. Amma gaskiya bana bugawa, don babu lokaci. Kuma Mamana ba ta so ina yi, don tana gani kamar wasan maza ne ba na mace ba. In ma ta ga ina yi sai ta yi ta faɗa ko ta ɗauke ƙwallon ta yi kyauta da ita. 

Ban da ƙwallon ƙafa akwai wasu wasannin motsa jiki da ki ke sha’awar yin su?

E. Ban da ƙwallon ƙafa ina kuma sha’awar wasan ƙwallon gora na Cricket, Kokawa irin na Wrestling, da kuma ƙwallon Kwando wato Basketball. Sai dai duk a cikinsu na fi son ƙwallon ƙafa.

Yanzu kina nufin kin daina bugawa kenan kwata-kwata? 

Yanzu kam gaskiya ba na yi tunda iyayena ba sa so, ko da kuwa ina son abin a raina. Sannan karatu ma ba zai bar ni ba, kasan na gaya maka ina zuwa karatun Islamiyya na Tahfiz, ba ni da lokacin kaina yanzu. Shi dama ƙwallo abu ne na nishaɗi, yanzu babu lokacin wasa. Kuma al’adarmu ta Arewa ba ta gamsu da ganin mace tana ƙwallon ƙafa kamar namiji ba, shi ya sa ko a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta matan Nijeriya za ka ga babu ƴar Arewa. 

A ƙungiyoyin wasan ƙwallon ƙafa na gida wanne kulob ki ke so?

Kulob ɗin da nake so shi ne Kano Pillars, masu gida! 

Shin kina bibiyar yadda wasannin motsa jiki na Olympic ke gudana a birnin Paris?

Wallahi ba na samun damar bibiya, saboda akasari lokacin da ake nunawa ba na gida, ko babu zarafin zama kallon.

Mene ne ra’ayinki kan rawar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Super Falcons ke takawa a wasannin da take bugawa?

Gaskiya ina jinjina musu sosai, bisa ƙoƙarin da suke yi, da yadda suke fitar da sunan mata a Nijeriya. Kuma ina matuƙar goyan bayan kulob ɗin sosai, saboda yadda suke ba da gudunmawa a harkar wasanni. Hakan yana sa kallon wasan su na ƙara shiga raina.

Shin kina ganin ya kamata iyaye musamman na Arewacin Najeriya su riƙa bai wa yaransu mata da ke sha’awar ƙwallon kafa, goyon baya?

Ina ganin ya kamata iyayenmu su riƙa la’akari da yadda zamani yake kawo abubuwa na sauye-sauye da dama. Yanzu harkar wasanni ta tashi daga nishaɗi da motsa jiki kawai hanya ce ta samun kuɗi. Idan mun lura za mu ga yadda ake samun wasu ƙasashen Musulmi da suke barin mata suna shiga wasannin motsa jiki. Sannan kuma kowa da baiwar da Allah Ya yi masa. Ba maza kadai ne ke da baiwar ƙwallo ba, Kina bibiyar wasannin ƙwallon ƙafa na ƙasashen Turai kuwa, kuma wanne kulob ki ke goyon baya?mata ma na da gudumawar da za su iya 

E, ƙwarai ina bibiya sosai, kuma ina matuƙar jin daɗin wasannin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasashen Turai. Wani lokaci muna kallo tare da yayana, ko na riƙa kallo a wayarsa. Ina ƙaunar wasan Real Madrid sosai. 

Ba kya fuskantar tsangwana daga wajen ƙawayenki ko samarinki game da yadda ki ke son ƙwallon ƙafa kamar namiji?

Wannan kam yana nan ba za a rasa ba. Yawancin mata sun ɗauki ƙwallo ƙafa a matsayin abin shirme. Wasu mazan kuma suna ɗaukar bai kamata a ga mata suna son ƙwallo ba,musamman a matsayinki na ‘yar Arewa kuma Bahaushiya. 

bayarwa. 

Banda ƙwallon kafa wanne abu ne ya fi baki sha’awa ki ga kina yi a rayuwarki?

Bayan sha’awar da nake da ita ta ƙwallon ƙafa, ina kuma sha’awar aikin jarida. Ina so in ga na zama fitacciyar ‘yar jarida mai gabatar da shirye-shirye da karanta labarai. Sannan kuma ina son kuma ina son in zama ɗaya daga cikin manyan marubutan Arewa. 

Shin za ki iya auren namijin da ba ya son ƙwallon ƙafa?

Gaskiya ba na ce ba, saboda ban san yadda ƙaddara za ta yi da ni ba. Amma a ra’ayina ina san na auri mijin da ya fi ni son ƙwallon ƙafa. Amma kuma zan iya aurar wanda ma ba ya so, matuƙar muna son juna. Abin na Allah ne. 

Mene ne shawararki ga sauran ƴan uwanki ƴammata masu sha’awar ƙwallon ƙafa kamar ke?

Ina so su cigaba da jajircewa da kuma addu’a, babu shakka sai da haƙuri da juriya ake kai wa ga matakin nasara.

Kina ganin ya kamata ƙungiyoyi irin su Kano Pillars su fito da ɓangaren ƴan mata, saboda ire-irenku masu sha’awar buga ƙwallon ƙafa, ko da ke ba ki shiga an yi da ke ba?

E, gaskiya a ganina ya kamata a samar da ƙaramin kulob na mata. Domin ƙara wa irin mu ƙwarin gwiwa da horar da mu. Ko da ni ba na ciki, amma ina kallonsu a matsayin ƴan uwana ƴan Nijeriya.

Yawwa, na gode.

Masha Allah. Ni ma ina godiya.

By ukarofi