Aliyu Mudi ya zama uban ƙasar Gorun Dikko na farko

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta amince da sake ƙirƙiro gundumar Gorun Dikko, tare da sababbin hakimai a waɗansu garuruwa a ƙarƙashin wasu gundumomi da ke ƙaramar hukumar Arewa.

Bayanin yana ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin masarautu, Alhaji Garba Umar Dutsinmari ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, 2026.

Takardar ta bayyana cewa an kuma amince da naɗa Alhaji Aliyu Mudi a matsayin Uban ƙasar sabuwar Gundumar Gorun Dikko da aka ƙirƙiro. Gundumar da aka sake ƙirƙirar ta ƙunshi garuruwan Hakimawa, Zamawa, Unguwar Sarki, Gorun Dikko I, Gorun Dikko II, Gigane da Landari.

Ta kuma bayyana cewa Gwamna Malam Nasir Idris ya amince da ƙirƙirar ƙarin hakimai a waɗansu garuruwa a ƙarƙashin gundumomi da ke ƙaramar hukumar Arewa da suka haɗa da gari ɗaya a ƙarƙashin Gundumar Gorun Dikko, garuruwa huɗu a ƙarƙashin Gundumar Jega, gari ɗaya a ƙarƙashin Gundumar Kangiwa, garuruwa biyu a ƙarƙashin Gundumar Chibike.

Takardar har wa yau ta bayyana cewa amincewar waɗannan naɗe naɗen an yi su ne bisa tanadin dokar ƙananan hukumomi ta jihar Kebbi ta 2008, musamman sashe na 10, sashe na (A) da (B), waɗanda ke bayar da damar ƙirƙirar gundumomi da naɗin hakimai.

Kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin masarautu, Alhaji Dutsinmari ya buƙaci sabon uban ƙasar na Gorun Dikko Alhaji Aliyu Mudi da sauran hakimawan su gudanar da ayyukansu da ladabi da kuma tsoron Allah da bayyana gaskiya da jajircewa, tare da tabbatar da cewa muradun al’ummarsu su ne a gaba.

By ukarofi

Leave a Reply