Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Al’ummar shiyyar Zamfara ta Arewa sun nemi hukumar kula da sadarwa ta Nijeriya (NCC) da ta dawo musu da netwok ɗin layukan waya waɗanda aka katse sama da watanni uku da suka wuce.
Mai magana da yawun ƙungiyar ƙaura Namoda Focus Forum (KNFF), Abdulrazak Bello, ne ya bayyana hakan a cikin wani jawabi da ya aike wa da Blueprint Manhaja.
Mr. Bello ya ce, rashin netwok ɗin ya shafi al’ummar ƙananan hukumomin Birnin Magaji, ƙaura Namoda, Shinkafi, da Zurmi waɗanda a jumulla yawansu ya kai miliyan 1.78.
Ya ce, kafanonin layi kamar MTN, Airtel da Glo sun dakatar da ayyukansu ba tare da yi wa al’umma bayani ba a hukumance.
Bello ya ƙara da cewa katse harkokin sadarwar ya fara gurguntar da harkokin kasuwanci da ilimi a yankin.
“Shiyyar Zamfara ta Arewa Allah ya albarkace ta da matasa masu ƙirƙira da basira da ke kasuwanci na zamani. Sannan akwai makarantar fasaha ta ƙaura Namoda da sauran manyan makarantu masu dama kuma dandali ce ta kasuwanci kamar ta manyan kasuwanni irin su Shinkafi da Kasuwar Daji da ‘yan kasuwa daban-daban a ciki da wajen Nijeriya ke zuwa domin saye da sayarwa.
“Katse sadarwa ta intanet a irin wannan wuri zai durƙusar da kasuwanci da ilimi da sa mutane da dama rasa ayyukansu da ƙaura wanda zai iya haifar da rashin tsaro da hatsaniya,” a cewar Bello.
Sauran mazauna yankin waɗanda suka zanta da Manhaja sun tabbatar da halin da ake ciki tare da neman NCC ta magance musu wannan matsala na rashin ɗaukar mataki da kamfanonin sadarwa suka yi.
Sun kuma zargi kamfanonin sadarwar da saɓa ƙa’ida da rashin mutunta haƙƙin al’umma da saɓa dokar NCC da ta wajabta hidimta wa al’umma yadda ya kamata.
“Al’umma ba kawai sun cancanci samar musu da netwok marar yankewa ba ne kaɗai har ma da sanar da su idan za a samu wata katsewa saboda suna da haƙƙin na sanin hakan da mutuntawa,” inji mazauna yankin.
Wani ɗan kasuwa, Umar Kaura, ya ce, matsalar sadarwa na shafar rayuwar al’umma mazauna yankin.
“Muna shan fama da rashin netwok na tsawon watanni. Wannan abu ne da ba mu taɓa tsammani ba. Ba ma iya shiga burauza mu duba intanet don sanin abin da ke faruwa ko kuma dandalin sada zumunta.”
“Idan ma an samu sabis, to ba shi da ƙarfi. Abin da muke iya yi shi ne tura sakon murya. An tauye mana ‘yancin samun bayanai da makamantansu.
“’Yan kasuwa a yankin ba sa iya sayen kaya daga Kano ko Legas saɓanin lokacin da muke da intanet. Wannan abin takaici ne saboda ba wanda yake magana a kan hakan. Wannan rashin netwok yana shafar rayuwarmu da ƙuntata mana a harkokinmu na yau da kullum,” inji Kaura.
Haka shi ma wani mai suna Sanusi Bashiru, daga garin ƙaura Namoda, ya bayyana cewa rashin netwok ya jefa rayuwar mazauna yankin cikin wani hali.
Ya ce ko data mutum ya saya baya iya yin komai da ita har sai in ya yi tafiya inda wa’adin kwanakinta ke ƙarewa ba tare da mutum ya amfana da ita ba.
“Yanzu mun koma rubuta saƙo ta hanyar takarda da biro ga mutanen da ke nesa da mu. Mazauna yankin na yin asara mai yawa saboda rashin netwok,” Bashiru ya faɗa.
Har izuwa yanzu dai mai magana da yawun NCC, Nnena Ukoha, ba ta amsa kiran wayarmu ba kuma ba ta turo amsar saƙon kar-ta-kwana da muka tura mata ba kan katsewar sadarwar intanet a yankin.
