Ambaliya: Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi jihohi 11

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta fitar da saƙon gargaɗi ga al’ummar jihohi 11 sakamakon yiwuwar samun mamakon ruwan sama a tsakanin ranakun Lahadi da Alhamis, lamarin da ka iya haddasa ambaliya da ɗaiɗaita mazauna da gidaje.

Cibiyar Gargaɗin Ambaliya akan Lokaci ta Ƙasa (NFEWC) ƙarƙashin Ma’aikatar Kula da Muhalli, ta bayyana jihohin da ambaliya ka iya aukuwa a wasu yankunansu. Jihohin sune: Adamawa, Benuwai, Nasarawa, Taraba, Delta, Neja, Kebbi, Kano, Katsina, Sokoto, da Zamfara.

A cewarta, yankunan sun haɗa da:
Adamawa: Ganye, Natubi
Benuwai: Abinsi, Agyo, Gogo, Ito, Makurdi, Udoma, Ukpiam
Nasarawa: Agima, Rukubi, Odogbo
Taraba: Beli, Serti, Donga
Delta: Umugboma, Umukwata, Abraka, Aboh, Okpo-Krika
Neja: Rijau
Kebbi: Ribah
Kano: Gwarzo, Karaye
Katsina: Jibia Sokoto: Makira Zamfara: Kaura Namoda, Shinkafi, Maradun, Gusau, Anka, Bungudu

Haka kuma, saƙon ya bayyana cewa kogunan Gongola, Benuwai da Neja ka iya cika da taimaka wa bazuwar ambaliya cikin sauƙi.

Don haka, ma’aikatar ta kirayi al’umma a yankunan da su ƙaurace zuwa wasu yankuna marasa barazanar samuwar ambaliya yayin da hukumomin agaji ke cikin shirin ko-ta-kwana.

By Babaji