Amurka da Chana za su warware zaren gabar da ke tsakaninsu

Shugaba Joe Biden, wanda ke zantawa da takwaransa Xi Jinping, ya ce akwai buqatar Amurka da Chana su gindaya wa kansu wasu ƙa’idoji don ganin cewa ƙasashen biyu sun kauce wa faɗawa mummunan rikici a tsakaninsu. Saɓanin da ƙasashen biyu suka jima suna fama da shi ya samo asali ne daga batun kasuwanci zuwa na kare haƙƙin bil adama.

A jawabinsa lokacin wannan tattaunawar wadda aka yi ta hoton bidiyo, shugaba Biden ya shaida wa takwaransa Jinping cewa, bai kamata gasa da lasashen biyu ke yi ta rikiɗe zuwa gagarumin rikici ba.

Biden ya ce, tabbas akwai ɗimibin batutuwan da suka haifar da rashin jituwa tsakanin Amurka da Chana da suka haɗa da sha’anin kasuwanci, makomar yankin Taiwan da kuma batun kare haqqin ɗan adam, to amma dukkaninsu batutuwa ne da ƙasashen biyu za su iya samar da maslaha a tsakaninsu.

A na sa ɓangare kuwa, shugaba Xi Jinping ya ce, akwai buƙatar Amurka ta ƙara inganta mu’amalarta da Chana lura da cewa ƙasashen biyu aminan juna ne da ke da daɗaɗɗiyar dangantaka.

Tattaunawar wadda aka fara da misalin ƙarfe 12 da mintuna 45 na daren da ya gabata, ta share tsawon awanni ana gudanar da ita, a cewar Jen Psaki kakakin fadar shugaban Amurka ‘White Housep, yayin da Ma’aikatar Harkokin Wajen Chana ke cewa shugabannin biyu sun tattauna a game da dukkanin batutuwan da suke da saɓani a tsakaninsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *