Amurka da Nijeriya na dab da cimma yarjejeniyar tsaro don yaƙar Boko Haram da ISIS 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Dan majalisar wakilan Amurka, Riley Moore, ya ce Amurka da Nijeriya na dab da cimma matsaya kan wani tsarin tsaro na dabaru da nufin yaƙar Boko Haram da ISIS a Nijeriya.

Moore, wanda ya kai ziyara Nijeriya tare da wasu ’yan majalisar Amurka, ya bayyana cewa sun yi tattaunawa masu kyau da gwamnatin Nijeriya kan batutuwan tsaro.

Ya ce ziyarar ta ba shi damar ganawa da wasu daga cikin waɗanda ta’addanci ya shafa, inda ya ce abin da ya gani ya girgiza zuciya.

Dan majalisar ya kuma ce zai miƙa rahoto ga Shugaban Amurka, Donald Trump, domin bayyana hanyoyin da za a bi wajen haɗa kai da gwamnatin Nijeriya don kawo ƙarshen kashe-kashen da ake dangantawa da ta’addanci.

A yayin ziyarar, tawagar ta gana da Mai Ba da Shawara kan Tsaron ƙasa, Nuhu Ribadu, a Abuja, tare da ziyartar wasu al’ummomi a arewacin Nijeriya.

Moore na daga cikin ’yan siyasar Amurka da ke iƙirarin ana tsananta wa Kiristoci a Nijeriya, kuma a ranar 7 ga Nuwamba ya gabatar da ƙuduri a majalisar wakilan Amurka kan lamarin.

By ukarofi