Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
An kori ɗan ƙasar Italiya da Senegal kuma wanda ya fi kowa yawan mabiya a TikTok, Khaby Lame, daga Amurka saboda ci gaba da zama a ƙasar har bayan ƙarewar bizarsa.
Jaridar New York Times ta ce, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Amurka (ICE) ta tabbatar da cewa an tsare matashin mai shekaru 25 a ranar Juma’ar da ta gabata a filin jirgin saman Harry Reid da ke Las Vegas.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ICE ta ce Lame ya shiga ƙasar ne a ranar 30 ga Afrilu, amma ya wuce lokacin da aka ba shi izini a bizarsa. Lame ya shahara ne, saboda barkwancinsa ba tare da ya yi magana ba a bidiyo, kuma a halin yanzu yana da mabiya sama da miliyan 160 akan TikTok. Shahararsa ta sa ya yi fice a duniya inda a akan saka shi har a fina-finan Hollywood, tallace-tallace da kuma wani wasan kwaikwayo mai suna ‘Khaby Is Coming To America’, wanda aka nuna shi a Tubi.
Nan da nan labarin korar sa ya bazu a duniya abin da ya haifar da muhawara da kuma martani mai zafi. Wani mai sharhi da ya bayyana kansa a matsayin mai goyon bayan shirin ‘Gen Z Trump Bo Loudon’ ya ɗauki alhakin korar Lame, inda ya rubuta a shafin Twitter cewa: “Duk wani baƙon da ba bisa ƙa’ida ba yana buƙatar a fitar da shi. Lokacin da na gano babban tauraruwar TikTok, Khaby Lame, baƙon da ba bisa ƙa’ida ba ne mai gujewa haraji, na yi aiki tare da ICE na Trump don korar sa, an kama shi kuma an kore shi.”
Lame bai fitar da wata sanarwa ba, amma a ranar Litinin ya yaɗa wani bidiyo a Instagram da aka ga alamar yana Sao Paulo na ƙasar Brazil, wurin da aka tabbatar ya je bayan barin Amurka.
Tsohon lauyan Lame, wato Riccardo Lanzo, ya faɗa wa jaridar New York Times cewa, yayin da Lame ya kwashe lokaci mai tsawo a Amurka, akwai rashin tabbas game da takamaiman matsayinsa na biza.
