Daga AISHA ASAS
Kamfanin jiragen saman Air India ya tabbatar da ɗaya daga cikin jirginsu, Flight 171, wanda ke kan hanyar zuwa London Gatwick daga garin Ahmedabad a yammacin Indiya, ya faɗi cikin wani mummunan haɗari da ya girgiza zukata.
Shugaban kamfanin, Natarajan Chandrasekaran, ya fitar da sanarwa cikin damuwa da alhini, yana cewa:
“Cije da alhini da baƙin ciki, ina tabbatar da cewa jirginmu Flight 171 daga Ahmedabad zuwa London Gatwick ya haɗu da wani mummunan haɗari a yau.”
Ya ci gaba da bayyana cewa:
“Zukatanmu da addu’o’inmu na tare da iyalai da dangi da duk waɗanda wannan musiba ta shafa. Wannan wata rana ce mai duhu ga kamfaninmu da ma dukan ƙasar.”
Wani jami’in filin jirgin saman Ahmedabad ya bayyana wa kamfanin labarai na AFP cewa, jirgin yana ɗauke da fiye da fasinjoji 200 a lokacin da lamarin ya afku. Wannan na nufin kusan a cike yake, duba da cewa Boeing 787-8 Dreamliner kan iya ɗaukar fiye da hakan.
Hukumar Air India ta ce ta buɗe cibiyar gaggawa tare da kafa ƙungiyar tallafi domin taimaka wa iyalan da ke neman bayani ko taimako dangane da danginsu da ke cikin jirgin.
Har zuwa yanzu, ba a bayyana ainihin dalilin haɗarin ba, kuma jami’an tsaro da hukumomin bincike sun shiga aiki domin gano musabbabin aukuwar wannan iftila’i.
A halin yanzu, al’umma daga sassa daban-daban na duniya na cigaba da nuna alhini da kuma taya iyalan fasinjojin addu’a, yayin da ake sa ido kan cigaban bayani daga hukumomi.
