Amurka ta takaita ba wasu ‘yan Afirka ta Kudu bizar shiga ƙasar

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Amurka ta sanar da sabbin takunkumin biza kan wasu ‘yan ƙasar Afirka ta Kudu, matakin da ke ƙara nuna tabarbarewar dangantaka tsakanin Washington da Pretoria a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Donald Trump.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ne ya bayyana matakin a ranar Talata, inda ya ce sabon tsarin zai shafi wasu ‘yan ƙasar Afirka ta Kudu da ake zargi da hannu ko haɗin kai wajen ƙirƙira ko aiwatar da dokoki da manufofin da ke ba da damar ƙwace filaye ba tare da diyya ba, nuna wariyar launin fata, ko tunzura tashin hankalin da ke gab da faruwa kan wasu tsirarun kabilu ko masu wani launi na fata.

Rubio ya ce gwamnatin Afirka ta Kudu ba ta magance damuwar da Washington ta riga ta gabatar mata ba, amma bai bayyana sunayen mutanen da sabbin takunkumin bizar za su shafa ba.

Matakin ya zo ne bayan watanni ana samun sabani tsakanin gwamnatocin ƙasashen biyu kan wasu manufofin Afirka ta Kudu, musamman batutuwan da suka shafi daidaita bambancin launin fata, rabon filaye da kuma ƙarar da Pretoria ta shigar kan Isra’ila a Kotun ƙasa da ƙasa ta Shari’a, wadda ta shafi yaƙin Gaza.

Gwamnatin Shugaba Cyril Ramaphosa ta musanta cewa akwai wata manufar nuna wariya ko tsananta wa fararen fata a ƙasar. Pretoria ta ce babu hujjar da ke nuna cewa ana nuna wa fararen fata wariya ko tsanantawa, tana mai cewa akasin haka, ra’ayoyin da ke ɗaukaka fifikon fararen fata na iya zama barazana ga haɗin kan Afirka ta Kudu bayan kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata.

Ramaphosa ya kuma yi kira da a ƙara ƙoƙari wajen karyata labaran da ya ce suna yaɗa zargin cewa ana tsananta wa fararen fata a ƙasar.

Wannan ba shi ne karon farko da gwamnatin Trump ta ɗauki matakan da suka shafi dangantakarta da Afirka ta Kudu ba. A baya, ta rage tallafin da take bai wa ƙasar, ta ba wasu fararen ‘yan Afirka ta Kudu damar neman mafaka a Amurka, sannan ta kori jakadan Afirka ta Kudu daga Washington.

Trump ya kuma sha yin ikirarin cewa fararen fata a Afirka ta Kudu na fuskantar wani yanayi na tsanantawa da kisan gilla, ikirarin da gwamnatin Afirka ta Kudu ta musanta.

By ukarofi

Leave a Reply