An ƙaddamar da kwamitin taimakon marayu a masallacin Sheikh Hassan Zango

Spread the love

Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi 

Domin magance matsalar wahalar da yara marayu da marasa galihu ke fuskanta a cikin al’umma, masallacin Juma’a na Abdurrahman Bin Awuf da ke zango Bauchi ya ƙaddamar da kwamitin mutane shida don lura da yadda za a rika tallafawa ta hanyar ba su ilmi da abinci da kulawar da ta dace.

Limamin masallacin Juma’a na Zango Imam Hussain Usman Zango, shine ya jagoranci ƙaddamar da kwamitin a karkashin jagorancin shugabannin kwamitin marayun masallacin gwallaga Malam Inuwa Ibn Ali da Malam Danjuma Bandas.

Wasu daga cikin shugabannin babban kwamitin marayun akwai Malam Yahaya Garba Sakataren kuɗi da mataimakin Sakatare shafiu Adamu Sai Dr. Jibrin Yamrat da Kuma Malam Labaran Mohammed Mainama.

Sakataren ƙungiyar JIBWIS reshen masallacin gwallaga Malam Danjuma Bandas cikin jawabinsa ya bayyana cewa yanayi ne ya sabbaba dole a fito da hanyoyin taimakon marayun,  shi yasa kungiyar jama’atu Izalatil bidah wa ikamatis Sunnah reshen gwallaga ta kirkiro kwamitocin 18 don taimakon marayun da ke karamar hukumar Bauchi.

An ƙaddamar da kwamitin marayu a unguwar Zango federal low-cost da ke Bauchi domin lura da dukkan lamurran inganta rayuwar yaran da iyayen su suka.rasu.

Hakan zai taimaka wajen magance matsalar lalacewar tarbiyya da ake samu saboda matsalolin rayuwa na yau da kullum ya zamo wajibi a tunkari lamarin saboda a kullum iyaye na mutuwa ana samun yawaitar yara marayu.

Sheikh Hassan Usman Zango limamin masallacin Juma’a na Abdurrahman bn Awuf da ke zango shine ya kaddamar da kwamitin mai dauke da kusan mutane goma domin aiki da sauran mutane shida na farko da kuma tattara taimakon biyan bukatun yaran don kare tarbiyyar su don kar su lalace su zamo lalura cikin al’umma.

Shugaban babban kwamitin marayu na masallacin gwallaga da ke Bauchi Sheikh Muhammad Inuwa Ibn Ali cikin jawabinsa ya shawarci Jama’a su rika kai iyaye mata makaranta don su fahimci addinin musulunci su inganta zaman aure da tarbiyyar iyali saboda su yi hakurin rungumar maraiaicin da Allah ya jarrabe su da shi.

Don haka ya ja hankalin jama’a su fahimci yawan marayun a kullum yana yawaita saboda matsalolin yau da kullum. Don haka ne kungiyar ta ware mutane biyar a kowace unguwa,  saboda dauko marayu 500 daga Unguwanni don daukar nauyin karatun su kyauta a makarantu.

Za a raba marayu 500 daga rassa 18 na cikin garin Bauchi don daukar nauyin karatun su a muhimman fannonin ilmi.

Ya ce kuma ana neman Sama da naira Milyan 18 don daukar mikatin fara taimakawa marayun a karamar hukumar Bauchi a matakin farko.

Kuma kungiyar za ta sake daukar marayu 100 don koya musu sana’a saboda su tashi da iya dogaro da kai su samu abin yi tun suna kanana.

Sheikh Mohammed Bin Ali ya kara da cewa ba a nan aikin taimakon marayun ya tsaya ba har taimakon marayun da abinci da tufafi.

Shugaban kwamitin na Zango Malam Hashimu Yusuf da mataimakin sa Malam.Abdulwahab da Abubakar Yusuf da PRO Mohammed Hussain da Malam Labaran Mohammed duk an dauko su daga Unguwannin wannan yankin ne don su taimaka kan aikin.

Sheikh Hassan Usman Zango limamin masallacin zango, yace yadda aka kaddamar da shugabannin kwamitin marayun  a iya sanin sa dukkan su mutane ne da suka dace.

Kuma saboda yadda ake mutuwa a kullum daukar wannan tsari ya zamo wajibi don a taimaki marayu a rage gaba tsakanin yara marayu da marasa gata da yaran mawadata.

Don haka shi ma Malam Danjuma Bandas ya kars bayyana cewa nan bada jimawa ba kungiyar za ta tattara alkaluman marayu da ake da su saboda duk lokacin da ake bukatar taimaka musu a san yadda suke kai tsaye.

Shi ma daraktan Ilmi na kungiyar jama’atu Izalatil bidah wa ikamatis Sunnah reshen gwallaga Sheikh Mohammed Tahir Bakoji cikin jawabinsa ya bayyana cewa wannan tsari na kwamitin taimakon marayun yana da matukar muhimmanci Kuma Ko shakka babu za su sauke nauyin da aka dora musu kuma da fatar za su yi hakuri su ci gaba da bada lokacin su kan wannan aikin na taimakon marayun tare da hada kan dukkan musulmi don a gudu tare a tsira tare.

By ukarofi