Dag MUHAMMADU MUJITABA a Kano
A karon farko an ƙaddamar da wani sabon taki na gargajiya da ke cikin leda a zamanance wanda ba shi da illa ga muhalli, ƙasa, da lafiyar al’umma bayan an yi amfani da takin a gonaki a noman damina ko noman rani kamar dai yadda MD Eseni Ibiam Orji, shugaban kamfanin Natari Group da ya samar da takin ta hanyar bincike da haɗin gwiwar ƙasar Thailand a Nijeriya da ya bayyana a wajen ƙaddamar da takin a Kano.
Babban jami’in kula harkokin kasuwancin takin shiyyar Arewa maso Yamma, Alhaji Suleiman Saminu, ya ce an yi bincike mai zurfi kan wannan takin ta yadda baya haddasa kowacce irin cuta kamar yadda aka ce takin zamani na haddasa cutar Daji, makanta da dai sauransu wanda hakan ce ta sa ƙasashen Turai ba sa yadda a shigar musu da kayan amfanin gonar da aka zuba masa takin zamani a ƙasashensu.
Taron dai ya samu halartar ƙungiyoyin manoma da sauran masu ruwa da tsaki a harkar noma daga ƙananan hukomomin Kano 44 da sauran mahalarta maƙota inda suka bada shawarwari da miƙa ƙorafi kan yadda taron ya gudana don kawo gyara da za a samu ci gaban kamfanin a Nijeriya.
