An ƙalubalanci marubuta kan kula da haƙƙoƙin addini da al’ada a taron marubutan Jos

Spread the love

Daga HABU DAN SARKI Jos

Marubuta, manazarta da masu sha’awar rubuce-rubuce cikin harshen Hausa sun gudanar da wani taron ƙara wa juna sani wanda ƙungiyar marubutan Hausa ta Jos Writers Club ta shirya, domin ƙara wayar da kan mambobinta game da yadda za su inganta rubutun su. 

A yayin wannan taro wanda aka gudanar a Cibiyar Nazarin Harkokin Sadarwa ta Hamzury Innoɓation Hub dake cikin garin Jos, an tattauna kan yadda marubuci zai isar da saƙon da ke ƙunshe a cikin labarinsa ga mai karatu, wanda shugaban ƙungiyar Abba Abubakar Yakubu ya gabatar, da kuma yadda marubuci zai yi amfani da fasahar AI wajen tsara labari, wanda Mataimakiyar Shugaba Aisha Sani Abdullahi ta gabatar.

Sauran waɗanda suka gabatar da lacca a taron sun haɗa da Ummusalma Yahaya Isah wacce ta yi jawabi game da abubuwan da marubuci ke buƙata don gina ingantaccen labari. Sai kuma Tameem Garga, Sakataren ƙungiyar, ya gabatar da nasa kan yadda ake ƙirƙirar halayen taurarin labari.

An buƙaci marubutan su mayar da hankali wajen koyon ƙa’idojin rubutun Hausa da amfani da ingantacciyar Hausa cikin rubutun su a maimakon yin rubutu kara zube ba tare da kula ba. Sannan an shawarce su da su riƙa tuntuɓar magabatansu a cikin ƙungiyar da wajenta, domin neman shawarwarin su kan yadda za su inganta ayyukan su na rubutu.

Wani muhimmin ɓangare na faɗakarwar da aka yi shi ne batun kiyaye martabar al’adun Hausawa da koyarwar addinin Musulunci da sauran addinai, domin kaucewa fuskantar ƙorafi ko saɓa wa dokokin ƙasa, dangane da girmama addinin kowanne ɗan Nijeriya da ƙabilarsa ko al’adun sa na gargajiya. An bayar da wasu misalai na inda wasu marubutan suka samu ƙalubale bayan fitar da littattafansu waɗanda a ciki suka ambaci wata ƙabila ko gari, yayin da mutanen wannan yanki suka nuna ɓacin rai game da abin da suka kira yunƙurin ɓata suna.

Harwayau, an gargaɗi marubutan da yin rubutun batsa wanda ka iya gurɓata tarbiyyar matasa da ɓata sunan marubutan Hausa a idon duniya, da kuma uwa uba shiga cikin fushin ubangiji. An kuma koyar da marubuta yadda za su ci moriyar fasahar zamani ta AI wajen samun jigon yin rubutu, shawarwarin yadda marubuci zai samu dabarun warware wata sarƙaƙiya a cikin rubutun da yake yi, da kuma fitar da hoton bangon littafin sa da sauransu.

Marubuciyar littafin, ‘Hattara Dai Mata’, Hajiya Maryam Abdullahi Isa ta shawarci mahalarta kwas ɗin da su yi amfani da darussan da suka koya cikin rubuce-rubucen su, kuma su kasance masu yawan karanta littattafan wasu marubutan don su ma su ƙaru da abubuwan da wasu ke rubutawa, domin su ma su inganta nasu rubutun. 

A ƙarshen taron an raba satifiket na shaidar halartar kwas ɗin ƙara wa juna sani ga dukkan waɗanda suka yi rijista.

By ukarofi