
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Bianca Ojukwu a mtsayin babbar minister harkokin waje.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa daga kakakin shugaban Bayo Onanuga da ta tabbatar da nadin uwargidan marigayi madugun ‘yan awaren Biyafara da a ka yi wa ahuwa Odumegwu Ojukwu.
Dama Bianca Ojukwu ce karamar minista ma’aikatar gabanin daga darajar mukaminta da ya biyo bayan murabus din tsohon ministan ma’aikatan Yusuf Tuggar wanda ya tafi Bauchi don shiga takarar gwamna.
Kazalika shugaban ya kawo sunan Sola Enikanolaiye don zama karamin ministan harkokin wajen.
Enikanolaiye dai daga jihar Kogi ya rike mukamin mai taimakawa shugaba Tinubu na musamman kan harkokin waje.
Yanzu za a jira majalisar dattawa ta tantance sabbin ministocin biyu don fara aiki a sabbin muƙaman.
