“Shaharar Dan’anace ta sa ake saka shi a cikin jerin mashahuran makaɗan ƙasar Hausa”
Daga IBRAHIM MUHAMMAD
(Danmadamin Birnin Magaji)
2.1 Shago ya yi ritaya daga wasan dambe:
Kafin dakatawar ƙarshe a shekarar 1962 a garin Tambuwal Jihar Sakkwato; a shekarar 1958 Sardaunan Sakkwato Alh. Sir Ahmadu Bello Firimiyan Jiha Arewa a lokacin, da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar na III, da Sarkin Daura Abdurrahman suka yanke shawarar aika ma Shago da ɗandunawa saƙon hana su buga dambe a tsakaninsu (su Biyu Shago da ɗandunawa). Sarkin Musulmi Abubakar na III ya naɗa Abubakar Shago a matsayin Sarkin Danben Sarkin Musulmi. Shi kuma Dandunawa an naɗa shi Sarkin dambenn Mai Martaba Sarkin Daura AbdurRahman.
Kamar yadda aka gani a buɗewar wannan kanun labarai, a shekarar 1962, Shago ya sake samun aike karo na biyu, daga Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar na III cewa kada ya sake buga wasan dambe a rayuwarsa.
2.2 Dalilin dakatar da Shago daga wasan dambe:
Idan an ce an kashe mutum a wasan dambe, ba a nufin kisa na mutuwa ba, ana nufin dai hannunsa da guwaiwansa sun taɓa ƙasa saboda bugu na abokin karawar dambe. Wannan shi ne dokokin da wasannin dambe suka tanada a al’adance. Kuma wanda aka kashe yana iya ɗaukar fansa. A tarihin wasannin dambe da shago ya buga, an shedi shago ya kashe shahararrin ‘yan dambe sittin da shidda (66). Talatin da ukku (33) cikin sittin da shida (66) a kisa bisa ga al’adar dambe, Shago ya kashe su, kuma ba su ɗauki fansa a kansa ba, har ya bar duniya. Amma sauran mutane talatn da ukku (33) da Shago yab buge su, ba su motsa ba daga inda suka hwaɗi, sai aka ɗauke su gawa sai lahira. Wannan labari ya kai kunnen Mai Alfarma Sarkn Musulmi, jama’a sun koka masa da cewa shi hwa Shago bugu ya kai da azazza kamar yadda Dan’anacce makaɗinshi ya shaidar a cikin Bakandamiyar Dan’anace ta Shagon Bakura Shagon Mafara. Allah kaji ƙansu da gafara amin. Shago daman ya shahara ga sana’ar noma, da kiwo da saye-da sayar da dabbobi. Da aka hana shi dambe sai ya mayar da hankali ga saurann sana’o’insa.
2.3 Wafatin Shago 1914 zuwa 1988 (74):
Alhaji Abubakar Aliyu Bawa ‘Yarkofoji Shagon Bakura, Shagon Mahwara, na ɗan’anace mai hwashe hanji, ya rasu sanadin gajeruwar rashin lafiya da ya yi fama da ita a ranar Laraba 2 Nuwamba, 1988 a garinsu na ‘Yarkufoji, Bakura, Zamfara. Ya bar matan aure huɗu (4) Asma’u da Aisha da Hafsatu da Hadiza. Ya bar ‘ya’ya takwas (8) Maza biyu (2) Sani da Isah. Mata shidda (6). Mata Hindatu da Rabi da Luba da Aisha, Hafsatu Yabi. A lokacin da ake tattara bayann wanann maƙala yaransa biyar ke a raye, Hafsatu da Isah da Aisha sun rasu.
3.0 Waiwaye Adon Tafiya: Bitar ayyukan da suka gabata kan Muhammadu Bawa Dan’anace ‘Yartsakkuwa:
Masu iya magana sun ce waiwaye adon tafiya. Domin ƙawata wannan sharhi kan makaɗa ɗan’anace an ribantu da wasu wallafe-wallafen masana kan wannan ɗan taliki. Aikin da hannu ya fara kai gare shi shi ne na Gusau, 1996 inda aka kawo tarihin wannan makaɗi, aka kuma bayyana muhimman abubuwa game da fasaharsa da gudummuwarsa ga adabin baka na Hausa, da kuma al’adun Hausa. Daga cikin muhimman abubuwan da aka zayyano a cikin wannan sharhi akwai:
1. Bayyana shekarun ɗan’anace 1916 -1986
An ga asalin yadda ɗan’anace ya koyi kiɗa daga kawunsa
An ga kason waƙoƙinsa da kuma sanfurinsu
Akwai gidan Rediyon Tarayya na Kaduna a shekarar 1972, sun ɗauki wata tattaunawa da wannan mawaƙi wadda ita ma aka ribantu da ita a cikin wannan waiwaye. Tattaunawar ta ƙunshi tambayoyi da amsoshi daga bakin shi ɗan’anace kamar haka:
*Bayyana tsawon lokacin da ya fara barin gida zuwa garuruwa wajen waƙa.
*Haɗuwarsa da Shago.
*Yadda ya samu ɗaukaka ta fuskar waƙa.
Akwai Gidan Rediyo na Rima da ke Sakkwato a shekarar 1975
*Waƙoƙinsa na wasu fannin rayuwa da ba na dambe ba.
*Haɗuwarsa da Shago.
*Tarihin wasu taurarin da Dan’anace ya ambata a cikin waƙoƙinsa.
Akwai kundin digiri na farko da aka gabatar a shekarar 1977
Ibrahim Muhammad (1977) ya gabatar da aiki kan Waƙoƙin Nazari, Keɓaɓɓen Nazari Kan Waƙoƙin Dan’anace inda ya bayyana wasu daga cikin waƙoƙin da suka sa Dan’anace ya shahara a fagen waƙa. Wannan kundin ya shekara talatin da tara (39) zuwa yau. An gabatar da shi tun ɗan’anace yana da rai, amma bayan ya tsufa ƙwarai, ba jimawa ya yi wafati.
Akwai wasu ayyuka da suka ambaci ɗan’anace amma kai tsaye ba a kansa aka yi aikin ba. Misali duk ayyukn da suka shafi makaɗan Maza, to za a ambace shi a matsayin ɗaya daga cikin makaɗan Maza, haka nan duk aikin da za a yi kan ‘yan dambe, to za a ambace shi a matsayin makaɗin ‘yan dambe. Ana kuma ambatarsa a matsayin makaɗain manoma domin ya yi wa manoma da yawa waƙoƙi. Wasu daga cikin waƙoƙin Jama’a duk ɗan’anace ya taɓa su.
Hannu ya iya Jiki ya Saba: Waƙa a Taskar ɗan’anace:
Ayyukan da suka gabata musamman waɗanda aka ambata a lamba ta 2.0 waɗanda suka keɓanta ga makaɗa ɗan’anace duk sun bayyana tare da tabbatar da cewa shi Muzakkarin Makaɗi ne, shahararsa ta sanya ana saka shi a cikin jerin mashahuran makaɗan ƙasar Hausa. A cikin tattaunawar da gidajen watsa labarai suka yi da shi (a duba shafin rataye na tattaunawa) an ga cewa ya amsa tambayoyi da dama da aka yi masa dangane da rayuwarsa kamar haka:
4.1 Yaushe ka fara Kiɗa? ɗan’anace ya fara kiɗa yana da shekaru goma (10) a duniya wato shekarar 1922. Ya bayyana cewa a ƙauyukansu ya daɗe yana yi wa manoma waƙa. Yana kuma yin waƙoƙi irin na bukukuwan suna da aure da kaciya. Haka nan yana zuwa filin wasannin gaɗa na maza da ‘yammata yana kaɗa kurkutunsa domin nishaɗantarwa.
Rukkunan Waƙoƙinsa: Ga yadda wannan Waiwaye ya fahimci rukunin waƙoƙin Dan’anace
A. Waƙoƙin bukukuwan gargajiya na al’ada:
*Bukukuwan aure.
*Bukukuwan suna.
*Bukukuwan kaciya.
*Bukuwan buɗin daji.
*Bukukuwan sallah.
B. Waƙoƙin noma:
I. Waƙar Garba Na-Godi 1918-1993 (75)
Sunan wanda aka yi ma waƙa: Hon Alh Garba Na-Godi Ajiyan ‘Yartsakkuwa
Shekarar da aka yi waƙa: 1958
Muhallin Waƙa: ƙofar Gidan Alhaji Baƙo Ajiyan ‘Yartsakkuwa (ƙofar gidan mahaifin wanda aka yi wa waƙar)
Saƙon Mawaƙi/Waƙa: Yabon Gwarzontakar Manomi Garba na-godi
ii. Waƙar Twanka ƙanen Sule 19??
Sunan wanda aka yi ma waƙa Twanka.
Shekarar da aka yi waƙa 1962.
Muhallin Waƙa Garin Nasarawar Bakura.
Saƙon Mawaƙi/Waƙa: Zuga.
iii. Waƙar Duniya Magadinki Allah (Ya yi halin Maza) 19??
Sunan wanda aka yi ma waƙa Sarkin Noma ɗangido Badamma ɗan-gara, ‘Yartsakkuwa, Rabah, Sakkwato.
Shekarar da aka yi waƙa 1959.
Muhallin Waƙa ƙofar gidansa da ke Badammar ɗangara, ‘Yartsakkuwa.
Saƙon Mawaƙi/Waƙa Tauhdi ga masu sauraro.
iv. Waƙar Irin ɗangeda (Sai an sha wuya akan tuna Allah)
Sunan wanda aka yi ma waƙa: Lauwali ɗan-Halima ‘Yartsakkuwa.
Shekarar da aka yi waƙa: 1947.
Muhallin Waƙa: ƙofar gidan wanda aka yi ma waƙar.
Saƙon Mawaƙi/Waƙa: Gwarzontaka.
v. Waƙar Giyen Sarkin Anka Iro Na Garba ƙanen Ama
Sunan wanda aka yi ma waƙa: Iron na Garba ƙanen Ama.
Shekarar da aka yi waƙa: 1971.
Muhallin Waƙa: Gandun Sarkin Zamfaran Anka a Matseri.
Saƙon Mawaƙi/Waƙa: Salon Zuga.
