
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumomin Saudiyya sun sanya yaren Yarbanci acikin jaddawalin yaruka 34 da za a fassara huɗubar ranar Arfa da su a yayin aikin hajjin 2025/1446.
Haka ma akwai yaren Fullanci (Fula) da Hausa, waɗanda manyan yaruka ne da ake amfani da su a Nijeriya.
Ma’aikatar harkokin addinin a Makkah da Madina ta sanar da hakan a wata takarda a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar Harkokin Addini, Dakta Abdulrahman Al-Sudais, ranar Alhamis.
Ya ce, an yi hakan ne da nufin isar da saƙon huɗubar zuwa ga mutane aƙalla miliyan biyar a faɗin duniya.
Ya kuma ce, fadar shugabancin ƙasar ta duƙufa wajen hidimta wa addinin musulunci da musulmai gami da bada kulawa ga maniyyata da baƙi a manyan Masallatai biyun masu tsarki.
A ranar 9 ga watan Zi-al-Hijjah ne za gudanar da huɗubar, wadda ɗaya ce daga cikin kwanaki masu albarka.
Ga jaddawalin yarukan da za fassara huɗubar da su kamar yadda IntelRegion ta ruwaito:
“1. Arabic
- Urdu
- English
- French
- Indonesian
- Persian (Farsi)
- Hausa
- Chinese (Mandarin)
- Russian
- Bengali
- Turkish
- Malay (Bahasa Melayu)
- Spanish
- Portuguese
- Italian
- German
- Filipino (Tagalog)
- Amharic (Ethiopia)
- Bosnian
- Hindi
- Dutch
- Thai
- Malayalam
- Swahili
- Pashto
- Tamil
- Azerbaijani
- Swedish
- Uzbek
- Albanian
- Fulani (Fula)
- Somali
- Rohingya
- Yoruba”
