An bankaɗo asirin wani kamfanin Isra’ila da ya shahara wajen sauya zaɓen ƙasashe

Wasu kamfanonin yaɗa labaran ƙasashe, sun yi haɗin gwiwa wajen bankaɗo ayyukan wani kamfani da aka yi wa laƙabi da Team George wanda ya ƙware wajen murɗa zaɓe da kuma yada farfagandar da za ta tayar da tarzoma a zaɓuɓɓukan ƙasashen duniya.

Bayan kafar yaɗa labaran da ta gudanar ta gano cewa kamfanin na shirin Murɗa labarai sama da 30 afaɗin duniya, cikin ƙasashen da ke shirin zaɓe a baya-bayan nan.

Kamfanin mallakin tsohon sojan ƙasar ta Isra’ila Tal Hanan mai shekaru 50, ya ƙware wajen murɗa zaɓuɓɓuka ta hanyar shiga rumbunan tattara sakamakon zaɓen hukumomin zaɓe da kuma aringizo ko rage yawan ƙuri’a.

Kamfanin ya kuma ƙware wajen yaɗa farfaganda a kafofin sadarwa da ma na yaɗa labarai da shafukan yaɗa labarai na bogi dubbai da yake da su.

Kamfanin da aka yi wa laƙabi da Team Jorge ya fara janyo hankalin kafofin yaɗa labaran ƙasashen Jamus, Faransa da Spaniya, inda kuma suka yi gangami wajen bibiyar sa da gudanar da bincike har ma da fallasa ayyukan sa.

A cewar kafofin yaɗa labaran da suka gudanar da binciken, a yanzu wannan kamfani babban barazana ne ga ɗorewar dimokraɗiyya da ci gaban ƙasashe masu tasowa, a don haka ya dace a mayar da hankali wajen daƙile ayyukan sa.